Karancin Naira: Ku Guji Tashin Hankali, Ku Nuna Fushinku a Zaben Shugaban Kasa, Kwankwaso Ga Yan Najeriya

Karancin Naira: Ku Guji Tashin Hankali, Ku Nuna Fushinku a Zaben Shugaban Kasa, Kwankwaso Ga Yan Najeriya

  • Sanata Rabiu Kwankwaso ya nuna damuwarsa kan tashe-tashen hankulan da aka samu a sassa daban-daban na kasar kan manufar sauya kudi na CBN
  • Dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ya yi kira ga daukacin yan Najeriya da su kara hakuri da bin doka da oda
  • Kwankwaso ya shawarci al'ummar kasar da su nuna fushinsu a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu mai zuwa

Yan kwanaki kafin babban zaben Najeriya na ranar 25 ga watan Fabrairu, an samu tashe-tashen hankula a wasu sassa na kasar sakamakon karancin kudi da ake fama da shi a kasar wanda ya ki ci ya ki cinyewa.

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya nuna damuwarsa a kan wannan al'amari.

Kwankwaso
Karancin Naira: Ku Guji Tashin Hankali, Ku Nuna Fushinku a Zaben Shugaban Kasa, Kwankwaso Ga Yan Najeriya Hoto: Vanguard
Asali: UGC

A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, 16 ga watan Fabrairu, Sanata Kwankwaso ya yi kira ga daukacin al'ummar Najeriya da su guji mayar da martani na tashin hankali kan halin da ake ciki a yanzu.

Kara karanta wannan

CBN: Tinubu Ya Gabatar Da Babban Bukata 1 Bayan An Yi Zanga-Zanga Kan Karancin Naira a Fadin Najeriya

Mu nuna fushinmu a zaben 25 ga watan Fabrairu - Kwankwaso

Da yake kira ga jama'a da su zamo masu bin doka da oda, tsohon gwamnan na jihar Kano ya bukaci da su nuna fushinsu a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Har ila yau, ya yi kira ga jama'a da su ci gaba da nuna juriya, jajircewa da kuma zaunar da kasar Najeriya lafiya.

Kwankwaso ya ce:

"Na damu da rahotannin tashe-tashen hankula da hargitsin da aka samu a wasu yankunan kasar kan mawuyacin halin da aka shiga na manufar sauya Naira.
"Yayin da nake jaddada cewa manufar bata dace ba a wannan lokaci, ina kira ga daukacin yan Najeriya da su ci gaba da bin doka da oda, sannan su guji duk wani martani na tashin hankali. Ina mai kira ga dukkanmu da mu nuna fushinmu a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu. Mu ci gaba da daurewa, mu jajirce, sannan mu zaunar da kasarmu lafiya. - RMK."

Kara karanta wannan

Tattaunawa: Lauya Ya Shawarci INEC Kan Yadda Zasu Dakile Sayen Kuri'u

Jama'a sun yi martani

@RakaFatima ta rubuta:

"CGFR mai zuwa in shaa allah ❤️"

@Hlover3282 ya ce:

"Masha Allah madogu uban tafiya ubangiji Allah ya khai mu ranar zabe mukadama kuri'armu "

@UsmanSa16263394 ya ce:

"Masha Allah Allah ya bada nasara."

@khalidmahmud6 ya ce:

"InshaAllah kai zaka ci zabe."

Karancin Naira: Ku kara hakuri da gujema tashin hankali, Tinubu ga yan Najeriya

A gefe guda, Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC ya yi kira ga al'ummar Najeriya da su yi hakuri da halin da ake ciki sakamakon manufar CBN na sauya kudi cewa komai zai zo karshe nan ba da jimawa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng