Jam'iyyar APC Ta Zabi Ranar Gudanar Da Sabon Zaben Fidda Gwani A Taraba

Jam'iyyar APC Ta Zabi Ranar Gudanar Da Sabon Zaben Fidda Gwani A Taraba

  • Bayan kai ruwa rana har kotuna uku kan lamarin dan takarar gwamnan Taraba a APC, za'ayi sabon lale
  • Rigima ta barke tsakanin mambobin jam'iyyar APC tun lokacin zabukan fidda gwanin gwamna
  • Kotu ta yanke hukuncin watsi da Sanata Emmanuel Bwacha matsayin dan takara gwamnan jihar na APC

Uwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta sanar da ranar gudanar da sabon zaben fidda gwanin dan takarar gwamnan jihar Taraba a zaben 2023 da zai gudana.

APC ta zabi ranar Juma'a, 10 ga watan Febrairu, 2023 kamar yadda wasikar ya nuna.

Wannan ya biyi bayan shari'ar kotun kolin Najeriya na ranar Lahadi wanda ya yi watsi da Sanata Emmanuel Bwacha a matsayin dan takarar gwamnan jihar na jam'iyyar APC.

A wasika mai dauke da ranar wata, 2 ga Febrairu, 2023, Sakataren tsare-tsare na jam'iyyar, Sulaiman Muhammad Argungun, ya bayyana shugaban APC na jihar cewa za'a yi zaben fidda gwanin ne a filin kwallon Jolly Nyame dake Jalingo.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Fito, An Bayyana Gwamnan PDP Da Ya Taimaka Aka Kayar da Atiku Ranar Zabe

Taraba
Jam'iyyar APC Ta Zabi Ranar Gudanar Da Sabon Zaben Fidda Gwani A Taraba Hoto: @channelstv
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar wasikar:

"Mun samu hukuncin kotun koli kan shari'ar dake tsakanin Cif David Sabo Kente dss da Sen Emmanuel Bwacha... na ranar 1 ga Febrairu 2023, inda kotun kolu ta soke sakamakon zaben fidda gwanin yan takaran gwamna jihar Taraba, kuma ta bada umurnin gudanar da sabon zabe."
"Biyayya ga wannan umurni bisa dokar zabe na 2022, mun zabi tsarin zaben deleget don gudanar da zaben fidda gwanin."
"Zaben zai gudana ne a filin kwallon Jolly Nyame dake Jalingo, jihar Taraba ranar Juma'ar. 10 ga Febrairu,2023."
"Muna muku fatan alheri."

Gwaman Mai-Ci yana kamfe da ‘Shinkafa da Maggi’ domin a zabe shi a 2023

Wani bidiyo ya bayyana a dandalin sada zumunta na Twitter, inda aka ji Gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku yana kamfe a wani yanki na jihar Taraba.

Kara karanta wannan

"A Soke Wannan Zaben Ayi Sabon Lale" Kwamitin Kamfen Atiku Ya Yi Kira Ga INEC

Legit.ng Hausa ba ta iya tantance a ina aka dauki bidiyon amma, amma an ji Gwamna Darius Ishaku yana jawabi mai kama da kamfe.

Fiye da mutum 80, 000 suka kalli wannan bidiyo da wani Shehu Abdullahi ya daura a shafinsa na @ShehunGwandu.

Mutane da dama sun bayyana ra'ayinsu kan wannan bidiyo.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida