Kai Tsaye: Yadda Kamfen PDP Ke Gudana Yau A Sakkwaton Shehu

Kai Tsaye: Yadda Kamfen PDP Ke Gudana Yau A Sakkwaton Shehu

Tawagar yakin neman zabe kujerar shugaban kasan Najeriya a zaben 2023 na jam'iyyar adawa ta PDP ta shiga cibiyar daular Islamiyya a yau Talata, 31 ga watan Junairu, 2023.

Atiku ya isa filin kamfe

Dandazon jama'a sun cika filin Giginya yayinda suke sauraron zuwan Atiku

Dubunnan mabiya jam'iyyar PDP sun cika filin Giginya suna sauraron zuwan dan takararsu, Atiku Abubakar, da mataimakinsa Ifeanyi Okowa.

Ana ta wake-wake da rare-raye a filin.

Komai ya kankama don fara kamfen PDP a Sokoto

Komai ya kankama a filin kwallon Giginya inda taron kamfen neman shugaban kasa Atiku/Okowa zai gudana.

Atiku, Tambuwal sun kai ziyara fadar sarkin Musulmi

Bayan ziyara kabarin Shehu, Atiku, Tambuwal, Saraki da sauran jiga-jigan PDP sun kai ziyarar ban girma fadar mai alfarma Sarkin Musulmi, Abubakar Sa'ad.

Atiku ya bayyana cewa:

"Gabanin garzayawa filin kamfe don yakin neman zabenmu a cibiyar daular Islamiyya, na jagorancin kwamiti na wajen kai ziyarar ban girma fadar Sarkin Musulmi, Mai Alfarma Muhammad Sa’ad Abubakar III.

"Na gode masa bisa shawarin hikima da ya masu."

"Na kuma gode sarki bisa kyautan littafan da ya bani. Ina addu'a Allah ya cigaba da zuba masa albarka."

Atiku da tawagar kamfe sun ziyarci Hubbaren Shehu

Alhaji Atiku Abubakar tare da tawagar kamfen jam'iyyar PDP sun kai ziyara kabarin mujaddadi Shehu Usmanu Danfodio.

Wannan na cikin ziyarar farko da suka kai gabanin zuwa filin taro.

Atiku ya yi addu'a inda yace:

"Yanzun nan Tawaga ta da ni muka ziyarci hubbaren Shehu Uthman Dan Fodio. Allah ya kyautata makwancinsa."

Online view pixel