Tsohon Gwamnan APC Ya Maka ‘Dan Jam'iyyarsa a Kotu, Ya Ce Dole Ya Biya Shi N250m
- Dr. Kayode Fayemi ya shigar da karar Kayode Otitoju saboda wasu kalamai da ya yi game da shi
- Tsohon Gwamnan Ekiti yana zargin ‘dan siyasar da ci masa zarafi, ya bukaci ya biya sa N250m
- Fayemi ya na so kotu ta karba masa diyyar N250m a hannun gidan talabijin da ya yi hira da Otitoju
Abuja - Dr. Kayode Fayemi wanda ya yi Gwamna sau biyu a jihar Ekiti, ya shigar da karar Kayode Otitoju da gidan talabijin nan na Arise a gaban kotu.
Kamar yadda labari ya zo a Premium Times, Dr. Kayode Fayemi yana tuhumar tsohon ‘dan takaran Sanatan da ci masa mutuncin da aka yada a talabijin.
A wannan kara da ke gaban babban kotun jihar Ekiti, tsohon Gwamnan ya bukaci Otitoju ya biya shi diyyar Naira miliyan 250 saboda ci masa zarafi.
Haka zalika tsohon Ministan ma’adanan kasar yana neman gidan talabijin Arise ya biya Naira miliyan 250 saboda da kafar ‘dan siyasar ya yi amfani.
Fayemi ya dauki hayar Babatunde Oke
Lauyan da ya tsayawa Dr. Fayemi wajen shigar da wannan kara a kotu, Babatunde Oke ya bukaci a gaggauta janye wadannan kalaman na cin mutunci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ya ce baya ga janye kalaman, Fayemi ya bukaci a nemi afuwarsa a fili ta hanyar wallafa neman hakurin a manyan jaridu uku da ke Najeriya.
Lauyan ya ce dole a kuma ba tsohon Ministan hakuri ta kafofin sadarwa na zamani da yanar gizo.
Idan tsohon Gwamnan na Ekiti ya yi nasara a kotu, Alkali zai umarci wadanda ake tuhuma da su guji sake maimaita wadannan kalamai ko a wallafa su.
Daily Trust ta ce Oke yana neman Naira miliyan 20 daga hannun wadanda yake kara, sannan a hada masa da 10% na ribar da aka samu daga shari’ar.
Meya ya yi zafi haka?
Da aka yi hira da shi a gidan talabijin kwanaki, Otitoju ya fito yana cewa Fayemi ne babbar matsalar da jihar Ekiti take fuskanta, ya jefe shi da wasu zargi.
Otitoju wanda ya rike Kwamishinan yada labarai a jihar yake cewa tsohon Gwamnan ya hada kai da wani Alkali wajen hana Kayode Ojo samun takara a APC.
Rikicin PDP a Kebbi
Tsofaffin Ministoci da wasu manya a PDP sun tarbi Atiku Abubakar a Kebbi, amma labari ya zo cewa wasu jiga-jigan jam’iyyar hamayyar sun ja kafa da shi.
An ga su Janar Ishaya Bamayi (retd.), Manjo Janar Bello Sarkin Yaki (retd.) da ‘Yan takara irinsu Ibrahim Manga, Sani Bawa, Haruna Saidu a wajen kamfen.
Asali: Legit.ng