Gwamna Adeleke Ya Yi Martani Kan Kwace Kujerarsa Da Kotun Zabe Ta Yi, Ya Bayyana Matakin Da Zai Dauka
- Gwamnan Jihar Osun Ademola Adeleke ya bayyana hukuncin da kotun zabe ta yanke kan zabensa a matsayin 'barin shari'a'
- Adeleke, wanda a baya ya lashe zaben gwamnan Osun na ranar 16 ga watan Yuli ya sha alwashin daukaka karar zuwa kotu na gaba
- Gwamnan da aka saba gani yana cashewa ya bukaci magoya bayansa su kwantar da hankulansu yayin da zai yi duk mai yiwuwa don karbo nasararsu da a cewarsa kotun ta kwace
Jihar Osun - Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya bayyana hukuncin zaben gwamna da kotun zabe ta yanke a matsayin 'rashin adalci', ya sha alwashin zai garzaya kotun daukaka kara, rahoton The Punch.
Mai shari'a Tetsea Kume, yayin yanke hukuncin, ya bayyana cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta bi dokoki da bukatun dokar zabe.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Da ya ke martani kan hukuncin kotun zaben daga kauyensa na Ede, Adeleke ya soki hukuncin kotun da ta bawa Mr Adegboyega Oyetola nasara, ya kira shi 'rashin adalci ga abin da masu zabe suka zaba.'
Yayin da ya ke kira ga magoya bayansa su kwantar da hankalinsu, Adeleke ya sha alwashin daukaka kara a kotun gaba, yana mai cewa har yanzu shine halastaccen wanda ya lashe zaben ranar 16 ga watan Yuli.
Gwamnan cikin sanarwar da mai magana da yawunsa, Olawale Rasheed ya fitar kuma ya rattaba wa hannu, ya ce:
"Ina kira ga mutanen mu su kwantar da hankulansu. Za mu daukaka kara kuma za a yi adalci. Ina tabbatarwa mutanen mu cewa za mu yi duk mai yiwuwa don kwato nasarar mu."
Kotu ta tsayar da ranar yanke hukuncin karshe kan zaben gwamnan jihar Osun
A baya, kun ji cewa kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Osun ta tsayar da ranar 27 ga watan Janairu na shekarar 2023 domin yanke hukunci na karshe.
Wata takarda da aka lika a hanyar shiga cikin kotun ta ce za a fara zaman shari'ar ne misalin karfe 9 na safiya kamar yadda jaridar The Cable ta rahoto.
Adegboyega Oyetola, tsohon gwamnan na jihar Osun karkashin jam'iyyar All Progressives Congress, APC, da jam'iyyarsa sun shigar da kara kotun suna kallubalantar nasarar Ademola Adeleke na jam'iyyar PDP.
Asali: Legit.ng