Peter Obi Ya Fallasa Wani Babban Sirri 1 Game Da Kansa Da Abokin Takararsa Ahmed-Datti
- Peter Obi ya bayyana kansa da abokin takararsa Yusuf Ahmed-Datti a matsayin shugabanni a Najeriya wadanda ba su aikata rashawa
- Dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar Labour ya furta hakan ne yayin ralli da suka yi a Jos, babban birnin jihar Plateau
- A cewar Obi, kamar abokin takararsa, bai taba satar kudin gwamnatin Najeriya ba
Jos, Plateau - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour a zaben 2023, Peter Obi, ya ce shi da abokin takararsa Yusuf Ahmed-Datti ba su taba satar kudin gwamnati ba.
Daily Trust ta rahoto cewa tsohon gwamnan na jihar Anambra ya bayyana kansa da abokin takararsa a matsayin shugabanni wadanda ba a same su da rashawa ba a kasar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Bisa la'akari da yawan rashawa a tsakanin manyan jami'an gwamnati a Najeriya, Obi
Obi, yayin jawabin da ya yi yayin kamfen dinsa a ranar Juma'a 20 ga watan Janairu, ya ce bisa la'akari da yawan rashawa a tsakanin manyan jami'an gwamnati a Najeriya, sune mutanen da ya dace a zaba a zaben shugaban kasa na Fabrairu.
Obi ya kuma ce mutane da kungiyoyi da ke yunkurin zarginsa sai dai kawai su ce shi marowacci ne.
Ya kara da cewa babu ko mutum daya da ya yi nasarar danganta shi da rashawa.
Yayin da ya yi alkawarin gwamnati mara rashawa, tsohon gwamnan na Anambra ya bawa mutanen kasar tabbacin cewa za a tsare kadarorin kasar idan an zabe shi shugaban kasa a zaben na Fabrairun 2023.
Ya kuma bada tabbacin cewa za a yi amfani da kudin kasar don amfanin talakawar Najeriya.
Asali: Legit.ng