Kai Tsaye: Yadda Taron Kamfen APC Ke Gudana Yau A Jihar Jigawa

Kai Tsaye: Yadda Taron Kamfen APC Ke Gudana Yau A Jihar Jigawa

Jirgin yakin neman kujerar shugaban kasan Najeriya a zaben 2023 na jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress APC ya garzaya jihar Jigawa, Arewa maso yammacin Najeriya.

Dan takarar shugaban kasan APC, Asiwaju Bola Tinubu; abokin tafiyarsa, Kashim Shettima; Shugaban uwar jam'iyyar, Adamu Aliyu da sauran jiga-jigai sun dira Dutse.

Sauran sun hada da gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu; Gwamnan jihar Jigawa, Muhammadu Badaru; Bashir Ahmed, dss.

Tinubu ya fara jawabi

TInubu yace:

"Idan zaku zabi shugaban kasa, ku zabe ni, ku zabi Jagaban, Allah ya muku albarka bayan kun zabe. Idan kuka zabe ni, kun zabi cigaba, kun zabi ingantaccen lantarki, kun zabi rayuwa mai kyau, ilmi mai inganci,
Idan zaku zabi Sanata, ku zabi na APC, idan zamu zabi na majalisar wakilai, ku zabi APC.
A ranar 11 ga Maris kuwa, ku fito ku zabi gwamna, ina rokonku, ku zabi APC
Zamu kawo karshen rashin zaman lafiya, zamu kawo karshen masu garkuwa da mutane, zamu karshen masu karban kudin fansa."

Tinubu ya isa farfajiyar kamfe

Sa'o'i biyu da dira Jigawa, Asiwaju Tinubu, ya isa wajen taron kamfen da aka shirya.

Dubunnan mabiya sun zagaye shahrarren dan siyasan.

Tinubu tare da Shettima, Badaru Talamiz, da sauransu sun shigo cikin mota mai budaddiyar sama.

Tinubu ya dira jihar Jigawa

Asiwaju Bola Tinubuya isa jihar Jigawa domin halartan taron yakin neman zabensa matsayin shugaban kasan Najeriya.

Tinubu, ya samu tarban manyan jiga-jigan jam'iyyar APC a jihar.

Online view pixel