2023: Kotun Koli Ta Sauya Dan Takarar Jam'iyyar APC a Jihar Kebbi

2023: Kotun Koli Ta Sauya Dan Takarar Jam'iyyar APC a Jihar Kebbi

  • Kotun Koli da ake wa lakabi da daga ke sai Allah ya isa ta yanke hukuncin karshe kan tikitin APC na majalisar tarayya a Kebbi
  • Kwamitin Alkalan Kotun karkashin Mai shari'a Uwani Abba-Aji, ta bayyana Mohammed Jega a matsayin sahihin ɗan takara
  • Kotun ta ce zaben fidda gwanin da Kabir Jega ya samu nasara ba NWC na APC ya shirya shi ba

Kebbi - Kotun Ƙoli a Najeriya ta rushe zaɓen Kabir Jega a matsayin ɗan takarar mamba mai wakiltar Jega-Aliero-Gwandu a majalisar tarayya na inuwar APC.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Kotun ta umarci a maye gurbinsa da Mohammed Jega a matsayin halastaccen ɗan takarar APC a mazaɓar ta jihar Kebbi.

Kotun Koli a Najeriya.
2023: Kotun Koli Ta Sauya Dan Takarar Jam'iyyar APC a Jihar Kebbi Hoto: premiumtimes
Asali: UGC

A hukuncin da Kotun ta yanke, kwamitin alkalai bisa jagorancin Uwani Abba-Aji, ta yi fatali da daukaka karar jam'iyyar APC mai goyom bayan Kabir Jega a matsayin ɗan takara.

Kara karanta wannan

NNPP Ta Ruɓe, An Bayyana Wanda Ya Kamata Kwankwaso Ya Janye Wa Takarar Shugaban Ƙasa a 2023

Legit.ng Huasa ta fahimci cewa APC ta miƙa sunan Kabir Jega ga hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) a matsayin ɗan takararta na majalisar wakilan tarayya a zaben 25 ga watan Mayu., 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma a ranar Jumu'a, Kotun Koli ta ayyana Mohammed Jega a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin da kwamitin ayyuka na APC ta kasa ya gudanar ranar 27 ga watan Mayu, 2022.

Kotun ta shure takarar Kabir Jega, wanda aka ce ya samu nasara a zaben fidda gwanin da aka gudanar ba kan doka ba.

A cewar Kotun dogaro da tanadin doka, NWC na jam'iyyun siyasa ne kaɗai ke da alhakin shirya zaben fidda gwani domin zaben dan takarar da zai fafata a babban zaɓe.

Mohammed Jega ne ɗan majalisar wakilai na mazaɓar yanzu haka, shi ne shugaban kwamitin 'yan gudun hijira, baƙi da masu neman mafaka a majalisa.

Kara karanta wannan

Kwanaki 35 Gabanin Zabe, Babbar Kotu Ta Kori Ɗan Takarar PDP Daga Shiga Zaben 2023

PDP ta shiga ruɗani a Imo

A wani labarin kuma Babbar Kotu Ta Kori Dan Takarar Majalisar Tarayya Na PDP a Jihar Imo

Kotun mai zama a birnin tarayya Abuja ta kori ɗan takarar PDP a mazaɓar tarayya kuma ta umarci a hanzarta shirya sabon zabe cikin kwanaki 14 masu zuwa.

Wannan ci gaban na zuwa ne kasa da mako ɗaya bayan Kotun koli ta soke tikin dan takarar Sanatan Imo ta yamma a inuwar PDP, Jones Onyereri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262