Tinubu Ba Musulmin Kwarai Bane, Yanzu Yake Koyon Abubuwan Addinin Saboda Siyasa - Dino Melaye

Tinubu Ba Musulmin Kwarai Bane, Yanzu Yake Koyon Abubuwan Addinin Saboda Siyasa - Dino Melaye

  • Dino Melaye, tsohon Sanatan Kogi, ya yi zargin cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na APC ba Musulmin kwarai bane
  • A wata wallafa da ya yi a ranar Litinin, 16 ga watan Janairu, Melaye ya yi ikirarin cewa Tinubu bai san muhimman abubuwa a addinin Islama ba
  • Sanatan ya ce a yanzu ne Jagaban yake kokarin koyon addini saboda dalilai na siyasa
  • Jigon na PDP ya fadi haka ne bayan ya saki bidiyoyi wanda a ciki ya kayar da Tinubu a gasar karatun Fatiha

Kamar yadda aka sansa da shirya dirama, Dino Melaye ya saki sakamakon abun da ya kira da gasar karatun Fatiha tsakaninsa da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

A wasu jerin bidiyoyi da ya saki a Twitter a ranar Litinin, 16 ga watan Janairu, Melaye wanda shine kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya bayyana yadda ya kayar da Tinubu a gasar.

Kara karanta wannan

Bayan Ganawa da Buhari, Gwamna Ya Bayyana Shugaban Kasa Mai Jiran Gado a 2023

Dino and tinubu
Tinubu Ba Musulmin Kwarai Bane, Yanzu Yake Koyon Abubuwan Addinin Saboda Siyasa - Dino Melaye Hoto: Dino Melaye, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Tsohon Sanatan na Kogi ya yi zargin cewa dan takarar shugaban kasa na APC ba Musulmin kwarai bane face wanda ke kokarin sanin wasu muhimman abubuwan Islama saboda dalilai na siyasa.

Melaye ya yi kira ga yan Najeriya da su yi waje da tsohon gwamnan na jihar Lagas a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya rubuta:

“Emilokan ba Musulmi bane illa Musulmin gaggawa da ke kokarin koyon muhimman abubuwa a Islama saboda dalilai na siyasa. Ku yi waje da shi.”

Dubban 'ya'yan APC Sun Fice Zuwa PDP a Jahar Bauchi

A wani labarin kuma, mun ji cewa a lokacin da babban zaben kasar ke kara gabatowa, jam'iyyar APC mai mulki a kasar ta rasa dubban mambobinta a jihar Bauchi.

Masu sauya shekar sun koma jam'iyyar PDP mai mulki a jahar bayan sun bayyana nasarorin da Gwamna Bala Mohammed na Bauchi ya samu a matsayin dalilinsu na komawa jam'iyyarsa.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Sanatan APC Ya Bayyana Yadda Kwankwaso Da Obi Ke Yi Wa Tinubu Aiki

Kamar yadda rahoto ya bayyana, mutanen sun sauya sheka ne daga fadin kananan hukumomi 20 na jihar.

Yayin da suke tabbatar da cewar za su yi aiki don nasarar jam'iyyar a zabe mai zuwa, sun bukaci PDP da ta tafi da su a harkokinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng