Dantakarar Gwamna Na Jam'iyyar APC a Jihar Kano Yace Bai Yadda Akwai Rashawa a Gwamnati Ba
- Kafar BBC Hausa ta gabatar da muhawara a tsakanin yan takarar gwamnan jihar kano su biyar
- A shekarar 2019 BBC Hausa ta fara shirya muhawarar a tsakanin yan takarar gwamna a jihohin Arewa
- A wannan shekarar ma kafar ta shirya yin muhawa a jihon arewa guda biyar wanda ta fara da jihar kano
Kano - Kafar BBC Hausa ta shirya muhawara a tsakanin yan takarar gwamna a jihar kano dan jin abinda yan takarar suka shirya yiwa jama'ar jihar kano.
Yan takara biyar BBC Hausan ta zaba, daga cikin yan takara sama da mutum 10 da suke neman kujarar gwamnan a jihar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wakilin Legit.ng Hausa ya rawaito cewa yan takara biyar din sun fito daga jam'iyyun PRP, PDP, APC, NNPP da kuma ADC.
Yan takarar daga kowacce jam'iyya Sune:
1. Sha'aban Sharada na jam'iyyar ADP
Sha'aban ya amsa tambayoyi daga daga wanda suka shirya da kuma mahalarta taron, daga cikin abin da sha'aban din yafi bawa fifiko a amsoshin tambayar da akai masa shine harkokin bunkasa kasuwanci da zuba hannun jari.
Sha'aban yace:
"Akwai kimanin yan kasuwa 150 daga kasashe 52 ne suke son zuba hannun jari a jihar kano idan dai yakai ga gaci."
Na daga cikin abinda Sha'aban din yace:
"Munyi magana da dan gidan sarkin Makka kan yadda zasu zuba hannun jarinsu a bangaren noma Akuyoyi a jihar Kano"
2. Nasiru Yusuf Gawuna na jam'iyyar APC
Gawuna ya maida hanakali ne kan ci gaban aiyukan da gwamnatocin baya sukai, tun daga kan Mallam Ibrahim Shekarau har zuwa kan Dr Abdullahi Umar Ganduje.
daga cikin wanda suka halarci muhawarar, Kabiru dakata ya tambayi dan takarar gwamnan kan baya ganin dakile rashawa da cin hanci kan iya samar da kudade masu yawa a gwamnati dan gudanar da wasu aiyuka?
Gawuna yace:
Nifa ban yarda akwai rashawa a gwmanati ba, idan akwai rashawa a nuna min"
3. Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP
Abba Kabir yusuf ya nuna a muhawarar cewa duk wani abu da tsohon gwamnan jihar kano Rabi'u Kwankwaso yayi to akansa zai dora.
yace duk wasu aiyuka da ake gani a gwamnati a karkashin gwamnatin Rabi'u kwankwason shine kashin bayan aikin, dan haka baya ganin akwai wani batu da zai masa wuya in ya kai ga gaci.
4. Muhammad Sani Abach na jam'iyyar PDP
Dan takarar jam'iyyar PDP da kwannan nan kotu ta tabbatar da shi, na daga cikin wanda suka halarcin muhawarar da BBC Hausa din ta shirya
Muhammad Abacha wanda yake dan kasuwa baiyi wasu maganganu masu yawa a wajen, yawancin abinda yafi maida hanakli a amsoshin tambayoyinsa shine a bari akai ga gaci tukunna, dan ganin hanyoyin da za'a bi dan magance matsaltsalun
Abacha yace:
"Duk abinda wadannan yan takara suke fada, abokin muhawarata Nasiru Yusuf Gawuna yace sunyi amma ba'a ga amfaninsu ba, dan haka in muka kai ga gaci zamu fito da hanya"
5. Salihu Tanko Yakasai
Salihu wanda yake tsohon mai hdimtawa gwanan jihar Kano Dr Abdullahi umar ganduje, ya nuna duk wasu tsari da kudiri da yayi niyyar yi ya riga ya dora su akan shafinsa, dan haka duk wani bayani da zaiyi to mutum zai iya zuwa ya duba.
Na daga cikin abinda da Dawisun ya maida hankali shine maida martani ga dan takarar ADP wato Mallam Sha'aban Sharada.
Dan takarar NNPP ya bar wajen muhawara, gabannin a kammala muhawara, sabida uziri da ya bayar na cewa zasu karbi tuta a jihar kaduna.
Mallam Ibrahim Isa na BBC Hausa shine ya jagoranci muhawara wadda aka shafe kusan awa biyu ana gabatarwa a babban dakin taro na cibiyar koyar da kasuwanci ta Dangote dake jami'ar Bayero a kwaryar birnin jihar kano.
Asali: Legit.ng