Kwankwaso Ya Samu Tagomashi A Ziyararsa Zuwa jihar Plateau
- Kwakwaso dai ya balle daga jam'iyyarsa ta PDP, inda ya dauko jam'iyyar NNPP kuma yake mata takarar shugabancin kasa
- Bayan dauko jam'iyyar dai masana sunce ta zama jam'iyyar ta hudu mafi zafin adawa da gwamnati a Nigeria
- Da yawa daga jiga-jigan jam'iyyar PDP, APC da sauran jam'iyyu ne dai sukai hijira suka koma jam'iyyar NNPP din
Plateau - Dubban dubatan jama'a ne sukai dafifin cicirindon ganin dan takarar shugaban kasa a jihar Plateau dake tsakiyar kasan nan wato arewa maso tsakiya.
Dr Rabi'u Musa Kwankwaso wanda yake wa jam'iyyar NNPP, takara ya samu tarbar ne a wannan larabar data gabata a garin Yalwan Shadam na karamar hukumar Yalwan Shedam na jihar.
Tsohon Ministan, tsohon gwamnan, kuma tsohon sanatan ya kai Ziyara ne ga sarkin yankin Miskoom Martin Madutre na III a fadarsa a Shandam. Rahotan The Cable

Kara karanta wannan
Zaben 2023: Dan Takarar Gwamna Ya Riga Mu Gidan Gaskiya, Jam'iyya Ta Maye Gurbinsa

Asali: UGC
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yayin da kwankwaso ke magana yayin ziyarar, yace ya mutukar jin dadi da yaba abinda al'ummar yankin sukai masa.
Kwankwasiyya Reporters sunce kwankwason na hanyarsa ne ta zuwa Bauchi daga jihar Plateau yayin da ya tsaya a fadar sarkin Shadem din.
Sun wallafa wani bidiyo mai dauke da yadda kwankwason ya ringa daga wa mutane hannu a garin na Shandem.
Jam'iyyar NNPP ta fasa kwai, wanda aka bawa takarar ya bada 500M
Shugaba jam'iyyar NNPP na kasa , Ahmed Rufa'i Alkali ya zargi dan takarasu na mataimakin gwamnan jihar Yobe da cin amana.
Jaridar The Nation ta rawaito Ahmed Rufa'i Alkali na cewa wani dan jam'iyyar NNPP ta ba takara ya saida tikitinsa, yayi watsi da zaben da za'a shiga a watan gobe.

Kara karanta wannan
Jami'an Tsaron DSS Sun Kama Tsohon Shugaban Yakin Neman Zaben Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam'iyyar LP
Jam'iyyar NNPP din ta garzaya hukumar zabe dan ganin ta cire sunansa daga cikin yan takarkarin hukumar, to sai dai hukumar taki.
Hakan yasa jam'iyyar garzaya gaban kotu a Abuja dan ganin hukumar ta amince mata da cire sunan dan takarar da take zargi da cin amanarta, kamar yadda ta fada.
Yau saura kwana arba'in da uku a gabatar da babban zaben Nigeria, wanda za'a zabi shugaban kasa, yan majalissar dokoki dana dattijai da kuma gwamnoni da yan majalissar su.
Asali: Legit.ng