Kotu Ta Soke Umarnin Kama Dan Takarar Gwamnan PDP a Jihar Akwa Ibom
- Kotu ta yi amai ta lashe a kan umarnin da ta ba Sufeto Janar na yan sanda, Alkali Baba inda ta bukaci ya kamo mata dan takarar gwamnan PDP a Akwa Ibom
- A yanzu kotu ta soke karar da aka shigar kan Umo Eno sannan ta dakatar da umurnin da ta yi na kamo shi kan zargin yaudara da ha’inci
- Ya ce tun farko wanda ya shigar da karar mai suna Edet Godwin ne ya jefa ta a duhu har ta kai ga zartar da hukuncin
Abuja - Wata kotun Majistare da ke Wuse 5, Abuja ta soke shari’a da umurnin kamu da ta bayar a kan Fasto Umo Eno, dan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Akwa Ibom.
Kotun ta kuma yarda cewa wanda ya shigar da kara, Wani mai suna Edet Godwin shine ya batar da ita har ta yi umurnin kama shi, jaridar Vanguard ta rahoto.
Fasto Umo Eno shine dai sahihin dan takarar jam’iyyar PDP mai adawa a kasar.
Yadda hukuncin ya samo asali
Tun farko dai mun ji cewa kotu ta umurci babban sufeto na yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba da ya kamo dan takarar gwamnan na PDP kamar yadda jaridar TheCable ta rahoto.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Babban alkalin kotun, Emmanuel Iyanna, ya bayar da umurnin kama Eno me bayan hukunta dan takarar gwamnan kan tuhume-tuhume da suka hada da yaudara da ha’inci.
Majiyoyi sun ce Eno ya ki halartan zaman kotu don haka aka yi shari’ar a bayan idonsa har aka kai ga yanke masa hukunci.
Zan daukaka kara kan hukuncin hana ni takara, Sanata Abbo
A wani labari na daban, sanata mai wakiltan yankin Adamawa ta arewa a majalisar dattawan Najeriya, Sanata Elisha Abbo ya sha alwashin kalubalantar hukuncin babbar kotun jihar da ta haramta masa yin takara a zaben 2023 karkashin inuwar APC.
Alkalin kotun dai ya ce Sanata Abbo bai da hurumin tsayawa takara a APC domin dai shugabancin jam'iyyar a karamar hukumarsa ta Mubi ta kore shi.
Da yake martani, Abbo ya ce kotu da ake ganin ita kadai ce gatan talka ta zama filin ciniki na ban gishiri na baka manda.
Asali: Legit.ng