Kotu Ta Tsige Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Ondo

Kotu Ta Tsige Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Ondo

  • Babbar Kotun jiha ta tsige mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Ondo, Hon Aderoboye Samuel daga kan mukaminsa
  • Wannan dai ya biyo bayan soke matakin mambobin majalisa na tube tsohon mataimakin kakaki, Hon Iroju Ogundeji
  • A watan Yuli, 2020, majalisar ta sauke Ogundeji daga matsayin mataimakin Kakaki kana ta amince da zaben Mista Samuel ya maye gurbinsa

Ondo - Babbar Kotun jihar Ondo mai zama a Akure, babban birnin jihar ta tsige mataimakin kakakin majalisar dokokin Ondo, Honorabul Aderoboye Samuel daga kan kujerarsa.

Kotun ta kuma umarci majalisar ta hanzarta maida, Honorabul Iroju Ogundeji a matsayinsa na mataimakin kakakin majalisar.

Gudumar Kotu.
Kotu Ta Tsige Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Ondo Hoto: thenation

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Kotun ta yanke wannan hokuncin ne bayan soke kudirin sauke Ogundeji daga kan mukamin mataimakin kakakin majalisar wanda mambobi suka amince a shekarar 2020.

Kara karanta wannan

Bayan Kotu Ta Haramta Masa Takara a 2023, Sanatan APC Zai Daukaka Kara

Honorabul Ogundeji, wanda ke wakiltra mazabar Odidbo ta 2 a majalisar, an tsige shi ne bisa zargin rashin da'a da rashin ladabi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bugu da kari, bayan sauke shi daga mukaminsa, majalisar ta dakatar da Ogundeji a watan Yuli, 2020 kuma duk wani yunkuri na maida shi bayan hukuncin Kotu ya ci tura.

Bayan haka ne zauren majalisa ya zabi Honorabul Samuel, mai wakiltar mazabar Odigbo II a matsayin sabon mataimakin kakakin majalisar dokokin.

Abinda hukuncin Kotun ya kunsa

Babbar Kotun ta umarci jagororin majalisar dokokin jihar Ondo su gaggauta maida Honorabul Ogundeji kan kujerarsa ta mataimakin shugaban majalisa.

Haka zalika Kotun ta umarci Aderoboye ya daina nuna kansa a matsayin mataimakin kakakin majalisa daga wannan rana da ta yanke hukuncin sauke shi, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Babbar Kotu Ta Kori Sanata Elisha Abbo Daga Matsayin Dan Takarar Sanata a APC

Kara karanta wannan

Ana Gab da Babban Zabe 2023, Shugaban Jam'iyya Na Jiha Guda Ya Yi Murabus, Ya Fadi Dalili 1

A wani labarin kuma Babbar Kotu mai zama Yola ta soke tikitin takarar Sanata Elisha Abbo a mazabar Adamawa ta arewa karkashin inuwar APC.

Kotun, karkashin mai shari'a Mohammed Danladi, ta ce tun a ranar 7 ga watan Oktoba, 2022, jam'iyar APC a gundumarsa da ke karamar hukumar Mubi ta kore shi daga inuwarta.

A cewar alkalin saboda haka Sanata Abbo bai da damar cin gajiyar da mambobin APC ke da ita, kuma ta umarci jam'iyar ta daina daukar Abbo a matsayin dan takararta a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262