Sulhu: Ya Zama Dole Aregbesola Ya Duka Ya Nemi Gafarar Tinubu – Tsohon Minista
- Gabannin babban zaben 2023, an bukaci ministan Buhari, Rauf Aregbesola, da ya duka ya baiwa jagoran APC na kasa, Bola Tinubu hakuri
- Tsohon ministan harkokin yan sanda, Jelili Adesiyan, ya ce lallai sai Aregbesola ya nuna nadamar abun da ya aikata kafin ya iya komawa daidai da Tinubu
- A cewar Adesiyan, shi baya kallon ministan a matsayin dan APC duk da cewar yana rike da mukami a gwamnatinta
Osun - Tsohon ministan harkokin yan sanda, Jelili Adesiyan, ya bukaci ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, da ya je ya nemi yafiya kan laifin da ya yiwa dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu.
Aregbesola dai ya yi cewa wasu yan siyasa na kokarin dakile kokarin sulhu da ake son yi tsakaninsa da Tinubu kamar yadda Premium Times ta rahoto.
Dole Aregbesola ya yi nadamar abun da ya aikata a jihar Osun
A wata hira da ya yi da jaridar Vanguard a garin Osogbo, Adesiyan ya ce tsohon gwamnan na jihar Osun ba zai koma daidai da dan takarar shugaban kasar na APC ba idan har bai yi nadamar laifukan da ya aikata a jihar ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce:
"Muna kira ga zaman lafiya kuma babu laifi a cikin sulhunta junanmu. Amma ko Allah ya bukaci masu laifi su nemi yafiya bayan sun yi nadama. A ganina, Aregbesola ba dan APC bane duba ga yadda ya yi abubuwa a zaben gwamnan jihar Osun da aka yi.
"Sulhu ba matsala bace; a kodayaushe shugabanninmu a shirye suke su karbi wadanda suka kauracewa jam'iyyar.
"Koda dai Aregbesola minista ne a karkashin gwamnatin APC, bai nuna jajircewa a matsayin dan jam'iyya ba. A kasa mai tunani, ba zai yi abubuwa yadda yake yi ba, amma a kulla yaumin shugabanci a shirye yake ya yi yafiya, amma akwai bukatar ya koma inda ya yi kuskure, ya ba da hakuri sannan ya nemi gyara ya kuma dawo tafarkin jam'iyyar.
"Aregbesola ya yi amfani da damar da shugabancin jam'iyyar ya bashi, musamman ma Asiwaju Bola Tinubu wanda ya kare shi daga wanda ba a sani ba zuwa gwamnan jihar Osun sau biyu, wajen hargitsa jam'iyyar da haifar da barasa tsakanin shugabannin jam'iyyar a jihar.
"Na san Asiwaju, kasancewarsa mutum mai zuciyar alkhairi, a shirye yake ya yafe masa, amma ya zama dole Aregbesola ya nuna nadama."
Za mu kasance masu amana tsakanina da Shettima - Tinubu
A wani labarin, babban jigon APC na kasa, Bola Tinubu ya sha alwashin cewa ba za su dunga cin mutuncin juna ba shi da abokin takararsa, Kashim Shettima idan suka hau kan karagar mulki.
Da yake jawabi a wani taron matasa, Tinubu ya ce ba za su dunga kwancewa juna zani a kasuwa ba kamar yadda tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo da mataimakinsa Atiku Abubakar suka yi.
Asali: Legit.ng