Datti Baba-Ahmed ya Zubda Hawaye kan Zagin Marigayin Mahaifinsa da Ake yi Bayan Shigarsa Siyasa

Datti Baba-Ahmed ya Zubda Hawaye kan Zagin Marigayin Mahaifinsa da Ake yi Bayan Shigarsa Siyasa

  • Mataimakin 'dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Datti Baba-Ahmad ya bayyana damuwarsa game da yadda abokan hamayyarsa suke cin zarafin danginsa, musamman mahaifinsa
  • Ya bayyana hakan ne yayin zantawa a wani shiri na The People's Townhall da aka yi shi kai tsaye daga Channels TV game da irin fafutukar da suke a siyasarsu
  • Yayi kokarin hana hawayen dake kokarin saukowa daga idonsu yayin da ya koka yadda ake zagin marigayin mahaifinsa da ya rasu shekaru 35 da suka shude

Mataimakin 'dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Datti Baba-Ahmad ya bayyana rashin jindadinsa game da tsokacin abokan hamayyarsa da suka yi na cin zarafi, musamman ga marigayin mahaifinsa.

Datti and Obi
Aikin 'Yan Sanda ba Bauta Bane, Jami'ai Zasu Iya Shan Giya a Mutunce, PPRO Legas. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

Yayin bada labari game da shirye-shiryen da suke na siyasa a The People's Townhall, wani shirin talabijin da aka yi kai tsaye daga Channels TV, mataimakin shugaban kasar jam'iyyar LP din, ya ce yayi aiki tukuru wajen yakar labaran karairayin da ake yadawa game da shi da marikin tutar jam'iyyar, Peter Obi.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Tinubu Ya Bincika Tarihin Peter Obi, Ya Nada Masa Sabon Suna

"A lokacin da na amshi tikitin, na tumbuke wasu karairayi game da shi, yayin da na hango inda suka dosa. Musamman takwarana a bangaren APC, wanda muke matsayi daya."

- A cewarsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Yayin da mutane suke tunanin suna da kudi, suna da mulki, sannan suna da iyayen gida, basu da mai taka musu birki. Dole sai wani ya tabo kafadarsu. Nayi hakan kuma na nuna yatsa. Idan ka kara- kayi daya, zan yi uku. Ka san zan aikata hakan.
"Sun dakata. Sai dai, ni da dangina mun amshi babban sakamako saboda yunkurin ceto Najeriya. Sun turo min mutane kala-kala."

Masanin fannin tattalin arzikin ya ce da "zai fi haka farin ciki" idan da a ce sukar ta tsaya kanshi shi kadai.

"Amma abun shi ne, nayi nasarar magance matsalar da abokan hamayyarmu na takarar shugaban da mataimakin, daga karshe na kare da jigatuwa a wani mataki kasa da wanda nake a da.

Kara karanta wannan

Na Sha Wahalar Kawai: Magidanci Ya Gane Dukkan Yaran da Matarsa ta Haifa ba Nashi Bane

"Shekaru talatin da biyar da suka wuce, a kalla, mahaifinmu mai girma ya rasu. Babu wanda ya taba zaginsa sai bayan na shiga takarar shugaban kasa. Hakan bai kyautu ba. Babu inda haka ke faruwa a ko ina a duniya ba.
"Bai kamata ka zagi iyayen mutane ko danginsu ba. Wannan ba abu bane wanda mutum zai iya jurewa ba."

- A cewar Baba-Ahmad, wanda kiri-kiri yayi kokarin hana hawayen dake kokarin saukowa daga kuncinsa kafin ya bar wurin zuwa wajen dakin shirya shirin, don ya samu natsuwa.

Ba jimawa ba ya dawo wurin zamansa don cigaba da tattaunawan a Channels TV.

Kotun daukaka kara ta jaddada Lawal Dare matsayin 'dan takarar gwamnan Zamfara

A wani labari na daban, wata kotun daukaka kara da ke zama a Sokoto ta ayyana Dauda Lawal Dare matsayin sahihin 'dan takarar gwamnan jihar Zamfara a karkashin jam'iyyar PDP.

Wannan na zuwa ne bayan da wata babbar kotun tarayya ta soke zaben da aka yin na fidda gwani tare da kwace takarar daga hannunsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng