Atiku Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro Da Satar Dukiyar Kasa Inji Tambuwal
- Shugaban yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP ne ke bayyana haka yayin yakin neman zabe
- Matsalar tsaro da satar ma'adanan kasa da kuma yin aiyukansu ba bisa ka'ida ba sun zama abinda yan siysa ke kamfen dasu, da zummar ganin sun kawo ci gaba kan harko hako su ko kuma zaman lafiya a kasa baki daya
- Atiku Abubakar na cikin mayan yan takarar da ke gaba -gaba wajen ganin sun kai ga gaci a zaben 2023
Sokoto - Aminu Waziri Tambuwal wanda yake a matsayin shugaban yakin neman zaben dan takarar jam'iyyar PDP yace muddin yan Nigeria suka bawa Atiku kuri'arsu to su sha kuruminsu kan batun matsalar tsaro
Tambuwal ya ce akwai ma'adanai masu yawan gaske a jihar Sokoto, wanda in aka amfanesu zasu kawo ci gaba mai yawa ga al'ummar sokoto da Nigeria baki daya.
Tambuwal na wannan maganar ne a yayin yakin neman zaben jam'iyyarsu ta PDP a karamar hukumar mulki ta Kebbe ta jihar. Rahotan jaridar Leadership
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jaridar Tribune ta rawaito cewa gwamnan na magana game da yadda ake hako ma'adanin gwal, tace gwamnan yace:
"Yadda ake tono gwal a yankin shine abinda ya kunna rikicin satar mutane domin neman kudin fansa, yan bindiga da kuma wasu matsal-tsalun tsaro da ake fama da su"
"Tambuwal ya ci gaba da cewa muddin aka bawa jam'iyyar PDP dama to an kawo karshen wannan batun, kuma duk wanda suke da hannu wajen satar dukiyar kasa suma za;a kawo karshensu.
Za'ai komai da tsari cikin mutuntawa da girmama juna
Gwamnan Sokoto yace wannan abubuwan duk da kuke gani na tono gwal da sauransu zamu sa hukumar kula da sa hannun jarin jihar Sokoto su sama muku lasisin da zau iya gudanar da aiyukanku ba tare da wata fargaba ba.
Amma fa hakan bazai yiwuba sai kun zabi jam'iyyar PDP, dan haka nake rokonku da ku daure ku zabi jam'iyyar PDP wadda Alhaji Atiku Abubakar ke mata takara muddin kuna so ku samu wannan ci gaban.
Kwana hamsin da daya ya rage a kada kuri'ar da zata bawa yan takara damar darewa kan madafun ikon da suke nema a matakin kasa da jihohi.
Asali: Legit.ng