2023: Matashiyar Da Ta Nemi Tikitin Shugaban Kasa Ta Samu Babban mukami a PCC
- Jam'iyyar SDP ta naɗa Khadijah Okunnu-Lamidi a matsayin mataimakiyar Darakta Janar na kwamitin kamfen 2023
- Khadijat, matashiyar da ta nemi tikitin takarar shugaban kasa ta nuna jin dadi da wannan mukami da aka ba ta
- Wannan na zuwa ne kasa da watanni biyu gabanin babban zaben 2023, wanda ake ganin shi zai fayyace goben Najeriya
Lagos - Social Democratic Party (SDP) ta nada Misis Khadijah Okunnu-Lamidi, a matsayin mataimakiyar Darakta Janar na Kwamitin kamfen shugaban kasa a zaben 2023.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Sakataren jam'iyyar SDP na ƙasa, Olu Agunloye, ya fitar ranar Talata 3 ga watan Janairu, 2023 a Legas.
Ya ce an naɗa Khadijah Lamidi da sauran mambobin PCC ne domin tabbatar da samun goyon bayan 'yan Najeriya masu kaɗa kuri'a gabanin babban zabe.
Hukumar dillancin labarai ta kasa NAN ta tattaro cewa Khadijah na ɗaya daga cikin 'yan takarar da suka nemi tikitin takarar shugaban ƙasa a SDP amma ta sha ƙasa a hannun Adewole Adebayo.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sakataren SDP ta kara da cewa Matashiyar ta tsaya tsayin daka a inuwar jam'iyar tare da nufin taka muhimmiyar rawa a kudirin ceto Najeriya da sake mata fasali.
SDP ta yi tunani mai kyau - Khadijah
Da take martani kan nadin da aka mata, Khadijah tace wannan matakin na ba ta mukami a PCC ya nuna cewa jam'iyar SDP na tafiya kan hanya madaidaiciya, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Misis Okunnu-Lamidi ta ɗau alkawarin aiki ba dare ba rana domin aiwatar da manufar dan takarar shugaban ƙasa a inuwa SDP na kare muradan talakawan Najeriya.
Tace:
"Na ji dadi matuka da wannan yarda da kwamitin gudanarwa ya nuna a kaina ya bani mataimakiyar DG a kwamitim kamfen da zai kai ga nasara."
"Na ji alfahari na samu damar yi wa kasata aiki da kuma jam'iyar SDP a yunkurinta na dawo da martabar mutanen mu da cika mafarkin Najeriya. Na shiga Kamfe ne don taimakawa a gyara yanayin da kasar nan ke ciki."
Manyan abu 2 da zasu faru da mu a 2023 - Oyetola
A wani labarin kuma Tsohon Gwamnan Osun Ya Faɗi Wanda Allah Yace Zai Zama Shugaban Kasa a 2023
Tsohon gwamnan Osun da PDP ta raba da madafun iko, Adegboyega Oyetola, ya ce Allah ya tsara faruwar muhimman abu 2 a 2023.
Oyetola yace Allah ya fada masa zai kwato hakkinsa da aka kwace masa kuma Bola Tinubu zai zama shugaban kasa a Najeriya.
Asali: Legit.ng