Yanzu Yanzu: Tsohon Mataimakin Gwamnan Jigawa, Gumel Ya Fice Daga APC

Yanzu Yanzu: Tsohon Mataimakin Gwamnan Jigawa, Gumel Ya Fice Daga APC

  • Shahararren jigon APC a jihar Jigawa, Ahmed Gumel, ya fice daga jam’iyyar saboda rikicin cikin gida da rashin hadin kai tsakanin ‘ya’yan jam’iyya
  • Gumel ya kuma yi korafi a kan rashin jajircewar jiga-jigan jam’iyyar a jihar wajen aiki don ganin sun yi nasara a zaben 2023
  • Idan har zarginsa ya zama gaskiya, hakan na iya shafar damar da Bola Tinubu na APC ke da shi a zabe mai zuwa

Jigawa - Ahmed Mahmoud Gumel, tsohon mataimakin gwamnan jihar Jigawa ya sauya sheka daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Gumel, wanda ya yi takarar tikitin gwamnan APC a zaben fidda gwanin jam'iyyar da aka yi a jihar a 2022, ya bayyana rikicin cikin gida da rashin hadin kan yan jam'iyya a matsayin dalilinsa na ficewa, jaridar Independent ta rahoto.

Kara karanta wannan

Rudani: Dalibin Aji 3 a Jami’a ya Gane Babu Sunansa a Rijistar Jami’a Baki Daya

Gumel da Tinubu
Yanzu Yanzu: Tsohon Mataimakin Gwamnan Jigawa, Gumel Ya Fice Daga APC Hoto: Independent/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Dalilin da yasa jigon na APC ya fice daga jam'iyyar

Jigon na APC ya bayyana hakan ne a wata wasika zuwa ga shugaban jam'iyyar, yana mai bayyana mutunci da kimar da jam'iyyar ke da shi a idonsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jawabinsa na cewa:

"Bisa dole na dauki wannan matakin saboda rikicin cikin gida, rashin hadin kai da rashin jajircewa da karfin gwiwa a manyan jam'iyyar wanda zai kai jam'iyyar ga nasara a zabe mai zuwa."

Gumel ya ba APC tabbacin ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki a jam’iyyar kan kowani tsare-tsare a gaba, ya yi wa daukacin ya’yan jam’iyyar fatan alkhairi, rahoton Daily Post.

Kafin zaben 2015, dan siyasan ya sauya sheka daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) inda ya koma APC.

Koda dai Gumel bai bayyana mataki na gaba da zai dauka a siyasarsa ba, akwai hasashe da ke nuna cewa yana iya komawa tsohuwar jam'iyyrsa ta PDP wacce ya bari a 2015.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP Ya Dauki Sabon Salo, Ayu Yana Kokarin Nunawa Tsagin Wike Iyakarsu

Me zargin Gumel ke nufi ga kudirin Bola Tinubu?

Ya bar APC ne a daidai lokacin da ake zargin cewa wasu gwamnonin jam'iyyar sun yi ganawar sirri da Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a Dubai.

Har ila yau, ficewar Gumel na iya zama barazana ga Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC a jihar Jigawa, idan har zargin da ya yi na cewar wasu shugbannin jam'iyyar basu jajirce wajenb ganin nasarar jam'iyyar a zaben 2023 ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel