Jam'iyyar PRP Ta Dakatar Da Ciyaman Dinta A Babban Jihar Arewa Saboda Rashawa

Jam'iyyar PRP Ta Dakatar Da Ciyaman Dinta A Babban Jihar Arewa Saboda Rashawa

  • Jam'iyyar PRP ta jihar Taraba ta sanar da dakatar da ciyaman din jihar Mr Abdullahi Maikasuwa
  • Sanarwar da Samuel Emmanuel ya fitar ta ce an dakatar da Maikasuwa na wata uku kan zargin rashawa da cin amanar jam'iyya
  • A bangarensa, Maikasuwa ya musanta aikata laifukan da ake tuhumarsa ya kuma bukaci al'umma su yi watsi da sanarwar

Jihar Taraba - Jam'iyyar People’s Redemption Party (PRP), ta ce ta dakatar da ciyaman dinta, Mr Abdullahi Maikasuwa na wata uku saboda rashawa da cin amanar jam'iyya.

Shugabannin jam'iyyar karkashin jagorancin Samuel Emmanuel yayin yi wa manema labarai jawabi a Jalingo, Nigerian Tribune ta rahoto.

Taraba PRP
Jam'iyyar PRP Ta Dakatar Da Ciyaman Dinta A Babban Jihar Arewa Saboda Rashawa. Hoto: Nigerian Tribune.
Source: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce sun tattauna kuma sun yanke shawarar nada Injiniya Idris Umar, ma'ajin jihar, ya yi aiki a matsayin ciyaman din jam'iyyar na Taraba har zuwa lokacin da kwamitin NWC ta yanke hukunci dangane da dakatarwar.

Kara karanta wannan

2023: Idan Atiku Ya Hau Mulki Babu Dan Najeriyan Da Zai Kara Kwana da Yunwa, Gwamnan PDP

A cewar shugabannin jam'iyyan, Maikasuwa, a lokuta da dama ya aikata rashawa da ayyukan cin amanar jam'iyya, inda ya rika yi wa mambobi barazana yana karbar kudi daga hannunsu.

Sun kuma zargi cewa Maikasuwa ya saba kundin tsarin jam'iyya ta hanyar tafiyar da harkokin jam'iyyar kamar kamfaninsa.

Wani sashi cikin sanarwar:

"Muna son sanar da cewa an dakatar da ciyaman din jam'iyyar PRP na jihar Mr Abdullahi Maikasuwa na wata uku har zuwa lokacin da sakatariyar kasa za ta yanke hukunci.
"An dakatar da shi ne saboda zargin rashawa da ayyukan cin amanar jam'iyya."

Martanin Maikasuwa

A bangarensa, Abdullahi Maikasuwa yayin martani ya musanta zargin rashawa da cin amanar jam'iyya da ake masa.

Maikasuwa ya kuma musanta cewa shugabannin jam'iyyar na jihar na da ikon dakatar da shi a matsayin ciyaman, yana mai kira ga al'umma su yi watsi da dakatarwar.

Mutanen yankin su Yakubu Dogara sun juya masa maya sun rungumi Bola Tinubu

A wani rahoton, mutanen yankunan Dass/Tafawa Balewa/Bogoro da ke jihar Bauchi sun fito sun bayyana goyon bayansu ga takarar Bola Ahmed Tinubu da sauran yan jam'iyyar APC a jihar.

Kara karanta wannan

AbdulJabbar: Yan Shi'a Sun Kai Karar Gwamnatin Kano Wajen Majalisar Dinkin Duniya

Mutanen yankunan da Yakubu Dogora, tsohon kakakin majalisar tarayya ke wakilta sun sha banban da ra'ayinsa na adawa da tikitin musulmi da musulmi na APC.

Sun bayyana cewa za su mara wa Tinubu baya ne saboda ayyuka da tsare-tsare da ya kawo a jihar Legas lokacin yana gwamna, suna son ya maimaita a matakin kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164