Za Mu Saka Matasa Su Yaki Yan Bindiga a Katsina - Dikko
- Gabannin zaben 2023, dan takarar gwamnan jam'iyyar APC a jihar Katsina ya bayyana matakin da zai dauka na yaki da yan bindiga a yankin
- Dr. Dikko Umar Radda, ya ce zai ba matasa horo da kayan aiki domin su taimakawa hukumomin tsaro wajen yaki da yan bindiga
- Hakimin Batsari, Alhaji Tukur Mu’azu Ruma, ya ce Dikko ne mutum na farko da ya kawowa yan gudun hijira agaji a yankin
Katsina - Dan takarar gwamnan jam'iyyar All Progressives Congress a jihar Katsina, Dr. Dikko Umar Radda, ya bayyana cewa zai yi amfani da matasa don yakar yan bindiga idan ya zama gwamnan jihar a 2023.
Dikko ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga dandazon jama'ar da suka fito don tarbar tawagarsa a yayin rangadin yakin neman zabensa a Batsari, daya daga cikin kananan hukumomin da ke fama da aikin ta'addanci a jihar, Vanguard ta rahoto.
A cewar mai neman zama gwamnan, za a horar da matasa, a basu kayan aiki sannan a tura su don taimakawa jami'an tsaro a yaki da yan bindiga a jihar.
Ya kuma ce wannan hanyar za a yi amfani da shi wajen yakar miyagu da kare yankunansu daga mahara.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Zan hana shanya rogo a kan hanya tare da samar da injinan aiki, Dikko
Dikko ya kuma yi alkawarin kawo karshen shanya rogo da ake yi a kan hanya a yankin ta hanyar samar da injinan da za su yi hakan cikin sauki, rahoton Independent.
Tsohon shugaban na SMEDAN ya kuma bayyana cewa takardar manufarsa ta tanadi hanyoyin bunkasa harkar noma ta hanyar samar da injinan noma wanda zai kawo riba ga manoma a yankin.
Dikko ne mutum na farko da ya fara kawowa yan gudun hijira agaji a Batsari
Da yake jawabi, hakimin Batsari, Alhaji Tukur Mu’azu Ruma, ya bayyana cewa dan takarar gwamnan na APC shine mutum na farko da ya tallafawa yan gudun hijira a yankin da tireloli biyu na kayan abinci a 2019.
Tukur ya ba dan takarar gwamnan tabbacin cewa da ace bai ziyarci yankin ba, mutanen Batsari za su yi masa kamfen da zabensa.
A wani labarin, Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya bugi kirjin cewa shine zai lashe zaben gwamna a karo na biyu a 2023.
Asali: Legit.ng