Gabannin 2023, Gwamna Inuwa Yahaya Ya Yi Alkawarin Gina Masallaci da Coci a Kauyen Todi
- Gwamnan jihar Gombe ya jaddada cewar shine zai sake lashe zaben gwamnan jihar a 2023
- A cewar Gwamna Inuwa Yahaya, abokan hamayyarsa na sauran jam'iyyun siyasa basa razana shi ko kadan
- A halin da ake ciki, gwamnan na jam'iyyar All Progressives Congress ya dau alkawarin gina coci da masallaci a kauyen Todi
Gwamna Inuwa Yahaya ya nanata cewa shine zai sake lashe zaben gwamnan jihar Gombe a 2023.
Yahaya wanda shine dan takarar gwamna na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar ya jaddada cewa babu mai iya ja da shi a tseren. A cewarsa, abokan hamayyarsa ba barazana bane ga kudirinsa na son zarcewa.
Za a ginawa al'umman Todi masallaci, coci da makaranta
Ya yi hasashen ne a wata hira da manema labarai bayan gangamin yakin neman zabensa a gudunma daban-daban na karamar hukumar Billiri da ke jihar, jaridar Leadership ta rahoto.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Da yake ci gaba da bayani a kauyen Todi, gwamnan ya yi alkawarin gina masallaci, coci a gudunmar bayan gabatar da bukatar hakan da mazauna yankin suka yi.
Ya kuma ce zai gina makaranta, hanya da gada a yankin Billiri ta arewa wanda ke fama da zaizayan kasa, jaridar Vanguard ta kuma rahoto.
Gwamna Inuwa Yahaya ya magantu a kan na'urar BVAS
A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Muhammad Inuwa Yahaya, ya ce ba ya tsoron matakin hukumar INEC ta dauka na amfani da na'urar tantance katunan zabe wato BVAS a zaben 2023.
Gwamnan na Gombe ya ce yan siyasan da basu da magoya baya sune suke fargabar sabon tsarin da hukumar zaben ta zo da shi.
Ya fadi hakan ne a wajen yakin neman zabensa wanda ya gudanar Garko, inda ya ce lallai talakawa na tare da shi har gobe.
A wani labari na daban, mun ji cewa yaran shugaban kasa Muhammadu Buhari, matamakinsa Yemi Osinbajo da Yusuf Bichi; shugaban hukumar DSS sun fito a jerin matasan da za su yiwa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na APC kamfen gabannin zaben 2023.
Sunayen Zahra Buhari, Yusuf Buhari, Kiki Osinbajo da Abba Yusuf Bichi sun bayyana a jerin sunayen da jam’iyyar APC ta fitar a makon nan.
Asali: Legit.ng