Majalisar Dattawa Ta Amince da Karin N819.5bn a Kasafin Kudi, Gwamnati Na Shirin Ciyo Karin Bashi
- Majalisar dattawa ta amince gwamnatin Buhari ta ciwo bahsin kudaden don cike gibin wasu ayyuka da aka fara a kasar nan
- An amincewa Buhari da karin N819.5bn a matsayin kari kan kasafin kudin 2022 da ke shirin karewa nan da gwanaki kadan
- 'Yan Najeriya na ci gaba da nuna damuwa kan kara hauhawar bashin da ake bin kasar tun daga hawan Buhari zuwa yanzu
FCT, Abuja - A ranar Laraba 28 ga watan Disamba ne majalisar dattawa ta amince da bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari na bukatar kari a kasafin kudin 2022 da N819,536,937,813.00.
Wannan na zuwa ne bayan da kwamitin majalisar karkashin Sanata Barau Jibrin ya duba fa’ida da alfanun wannan kari da Buhari ya nema, The Nation ta ruwaito.
Sanata Barau ya bayyana cewa, kudade da ake bukata za su yi amfani ne wajen karasa ayyukan da aka fara a kasar nan da suka hada da tituna da dama-daman ruwa da suka lalace a daminan bana.
Gwamnatin Buhari za ta sake cin bashin biliyoyin kudi
Hakazalika, ya ce gwamnati za ta samar da wadannan kudaden ne ta hanyar cin bashin cikin gida domin karasa wadannan ayyukan, Punch ta ruwaito.
Idan baku manta ba, shugaban kasa Buhari ya tura wasika ga majalisar ne a baya tare da neman a bashi damar sake cin bashi don karasa ayyukan da gwamnatinsa ta fara a shekarar 2022.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Amincewar majalisar na kara adadin kudin ya kara kasafin kudin zuwa N8.17trn; daidai da karin 4.43% kenan kan kasafin farko.
Hakazalika, kara cin bashin da Buhari zai kara adadin bashin da ake bin Najeriya a cikin gida a 2022 zuwa N3.33trn.
Don tabbatar aiwatar ayyukan da aka bayyana a cikin bukatar Buhari, majalisar ta kara wa'adin kammalar ayyukan karin kasafin kudin 2022 zuwa 31 ga watan Maris 2023.
Buhari ya fadi kudaden da ya kashe wajen gyara ofisoshin 'yan sanda da bariki a cikin shekaru 3
A wani labarin, gwamnatin Najeriya ta bayyana adadin kudaden da ta kashe wajen inganta ayyukan 'yan sanda a Najeriya.
Hakazalika, gwamnati ta fadi abubuwan da ta yi wajen gyara da gina barikin 'yan sanda da ofisoshi a fadin kasar.
Gwamnatin Buhari na yawan bayyana manufarta ta sake inganta ayyukan gwamnati.
Asali: Legit.ng