2023: El-Rufai Na So a Fara Hukunta Yan Siyasa Masu Ci Da Addini

2023: El-Rufai Na So a Fara Hukunta Yan Siyasa Masu Ci Da Addini

  • Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya bukaci a fara daukar mataki na hukunta yan siyasa da ke ci da addini
  • El-Rufai ya zargi wasu yan siyasa da amfani da addini da kabilanci don raba kan jama'a yayin yakin neman zabensu
  • Gwamnan Kadunan ya kuma nemi yafiyar dukkanin mutanen da ya sabawa gabannin barinsa kujerar shugabanci

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa akwai bukatar a fara hukunta yan siyasa da ke amfani da addini a matsayin makamin yakin neman.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 28 ga watan Disamba, yayin bude ofishin Gidauniyar Bunkasa Zaman Lafiya da Ci Gaba na Sarkin Musulmi, Daily Trust ta rahoto.

Ya nuna damuwa kan yadda wasu yan siyasa ke amfani da addini da kabilanci wajen raba kawunan jama'a a yakin neman zabensu.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi Ya Bayyana Abu 1 Da Yan Kaduna Ba Za Su Taba Manta El-Rufai a Kansa Ba

El-Rufai
2023: El-Rufai Na So a Fara Hukunta Yan Siyasa Masu Ci Da Addini Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Yan Najeriya za su samu damar kawo karshen masu ci da addini a 2023, El-Rufai

El-Rufai ya ce zaben 2023 zai ba yan Najeriya cikakkiyar damar fatattakar addini a siyasa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamnan na Kaduna ya kuma yi kira ga sarakunan gargajiya da malamai a kan su roki Allah ya zama shugaba nagari wanda zai hada kai da ciyar da kasar gaba a babban zaben da za a yi a watan Fabrairu.

Ya kuma yi kira ga sarakuna da malamai da su wayar da kan mutane kan bukatar tabbatar da ganin cewa makomar zabe bai karkata a kan addini ba maimakon haka ya kasance kan abun da mutum zai iya yi don inganta rayuwar talaka.

El-Rufai ya ce:

"Muna na hadaka a talaucinsu, a bukatar iliminsu, a kiwon lafiya da hanyar samun abincinsu, wannan shine ya kamata mu mayar da hankali a kai amma wasu mutane na haduwa don habbaka rabuwan kai a bangaren addini da kabilanci. Wannan shine abu na karshe da Najeriya ke bukata a lokaci da duniya gaba daya ke fuskantar kalubale."

Kara karanta wannan

Bidiyo: Fitaccen Malamin Arewa Ya Nemi Mutane Kar Su Zabi Wanda Zai Murkushe 'Yan Bindiga

Ya kuma roki yafiyar jama'a yana mai cewa:

"Muna kokarin aikata daidai amma Allah kadai ne ke daidai, ina mai ba da hakuri ga duk wanda na yiwa laifi, ya rage mana watanni biyar mu tafi kuma zan so na tafi sannan na yi bacci cikin nutsuwa."

Da yake jawabi a bangarensa Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ce gidauniyar na ta tattaunawa da masu ruwa da tsaki don ganin yadda za ta daukaka rayuwar al’umma, rahoton Aminiya.

Hakazalika, jagorar gidauniyar kuma Sarkin Argungu, Alhaji Samaila Muhammad Mere, ya jinjinawa gwamnan na jihar Kaduna kan kyautar fili da ya bayar don gina ofishin gidauniyar da kuma bayar da naira miliyan 25 don gina filin.

A gefe guda, sarkin Musulmi ya ce suna yiwa gwamnan na jihar Kaduna lakabi da babban mutum a lokacin da suke kwalejin Barewa duk da kankantar jikinsa saboda hangen nesansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng