Kyawun Rubutun Abokin Takarar Tinubu, Kashim Shettima Ya Jawo Cece-Kuce a Twitter
- Abokin takarar shugaban kasa ga Bola Tinubu ya lashe zukatan wasu a shafin Twitter da irin rubutunsa mai kyau
- A bangare guda, Kashim Shettima ya sha sukar wasu mutane daban kan yadda ya ke rubutu mai kyau da hannun hagu
- Rahoton da muka tattaro ya bayyana kadan daga abin da mutane ke cewa bayan ganin bidiyon rubutun Shettima
Wani bidiyon da ya yadu a kafar sada zumunta ya nuna lokacin da abokin takarar Tinubu a APC, Kashim Shettima lokacin yake cancara rubutu a wata takarda.
Sanata Kashim Shettima, wanda shine tsohon gwamnan Jihar Borno, ya ba da mamaki yayin da ya fito a matsayin abokin takarar Bola Ahmad Tinubu.
An ga rubutu mai kyau kuma mai daukar hankali, lamarin da ya dauki hankalin jama’ar Twitter da dama.
Festus Kayemo ya yada bidiyon a shafinsa na Twitter, inda yace ya rubuta kalaman fatan alheri ne ga sarkin Kazaure, mai martaba Alh. Dr. Najib Hussaini Adamu lokacin da ya ziyarce shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutane da yawa sun nuna sha’awa ga kyawun rubutun Shettima, sun yi martani a kan bidiyon.
Kalli bidiyon:
Martanin jama’ar Twitter
Ga kadan daga abin da mutane ke cewa game da bidiyon rubutun Shettima:
@kolaoyedijoSnr
“Bambancin a fili yake... ASIWAJU ba zai taba dauko dakiki ba a matsayin mataimaki, haka nan APC. Tinubu/Shetimma, hanya dodar zuwa Aso Rock a ranar 29 ga watan Mayu.”
@LeonardoOkojie
“Yanzu wasu za su fara suka a kan yana amfani da hannun hagu.”
@Frankasino
“PO zai ba shi aikin sanya hannu a kan satifiket din kammala ayyuka. Ya kware wajen iya rubutu mai kyau...”
@salisu_gwadabe
“Tabbas mai girma Sanata, kuma mataimakin shugaban kasa mai jiran gado insha Allah.”
@Mr_darni
“Shugabanmu, abin koyinmu..Allah ya shirya ya kuma kare ka ameen.”
@GabrielAwujoola
“Wannan mutumin haziki ne.”
@famonzo01
“Meye amfanin rubutun hannu mai kyau ga wanda dan ta’adda ne? Ina kalubalantarsa a gasar rubutun hannu. Kowa zai iya rubutu mai kyau da alkalami irin wannan.”
@Ibnbazo
“Da yawan masu rubutu da hannun hagu sun iya rubutu kuma wannan na daban ne.”
Bayan ganawa da Shettima, attajirin dan Najeriya kuma jigon Arewa, Dantata ya bayyana halin da yake ciki, ya ce duniya ta daina masa dadi.
Asali: Legit.ng