Har Yanzu Kai Korarre Ne a PDP, Wike Ya Maida Zazzafan Martani Ga Secondus
- Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya maida martani ga tsohon shugaban PDP na ƙasa da ya gabata, Uche Secondus
- Musayar yawu ta barke a tsakanin jiga-jigan ne bayan Wike yace a watan Janairu zai faɗi dan takarar da zai wa aiki a 2023
- Secondus ya yi ikirarin cewa babu wanda ya isa ya kakabawa mazauna Ribas ɗan takarar da zasu zaɓa
Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, yace tsohon shugaban PDP da ya gabata, Prince Uche Secondas, na nan a matsayin korarren mamba don haka ba shi da ikon tsoma baki a harkokinta.
Wike ya bayyana haka ne a wurin kaddamar da Titin Aluu-Omagwa, Omagwaa, ƙaramar hukumar Ikwerre ta jihar Ribas, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Gwamnan ya yi martani ne ga kalaman Secondus, wanda ya ce babu mahalukin da ya isa ya ƙaƙabawa mutanen Ribas ɗan takarar shugaban ƙasar da zasu zaba.
Tsohon shugaban PDP ya yi waɗan nan kalamai biyo bayan matsayar gwamna Wike, wanda ya sha alwashin ayyana ɗan takarar da zai wa aiki a watan Janairu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Gwamana Wike ya ce:
"Tsohon mamban jam'iyyar mu, Uche Secondus, yace ba wanda wuyansa ya isa ya kakaba wa mazauna Ribas wanda zasu zaɓa a kujerar shugaban kasa. Shi ba ɗan PDP bane, gundumarsa sun kore shi kuma Kotu ta tabbatar."
"Bayan korarsa daga PDP ya zarce Kotun ɗaukaka ƙara nan ma aka fyaɗa shi da kasa, yanzu yana Kotun Koli kuma za'a koma zama ranar 23 ga watan Oktoba, 2023."
"Na fada masa ba zai shirya babban taron PDP a matsayin shugaba ba, shin shi ya shirya? Kun gan shi a wurin taron? Har zuwa yanzu kai ba ɗan jam'iyya bane."
Ban ce zan kakabawa mutanen Ribas ɗan takara ba - Wike
Gwamna Wike, jagoran tafiyar G5, yace ba kakaba wa mutane ɗan takarar shugaban kasa ya ce zai yi ba, zai bayyana wanda zai wa kamfe ne a 2023.
"Ba cewa na yi zan kakabawa mutanen Ribas ba, abinda na ce zan bayyana wanda zan goyi baya, wanda zan yi wa kamfe, amma kar ku yi mamaki idan aka ce baka yi karatun Sakandire ba, ai ba zaka fahinta ba."
A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP ta gamu da babban cikar a jihar Daraktan kwamitin yakin neman zaben Atiku 2023
Alhaji Yusha'u Kebbe, da ake ganin yana ɗaya daga cikin ginshikan jam'iyyar PDP ya sauya sheka zuwa APC a jihar Sakkwato.
Ya bayyana cewa sai da ya tuntuɓi magoya bayan sa a dukkanin ƙananan hukumomi 23 na jihar kafin ya yanke wannan hukunci.
Asali: Legit.ng