Gwamnan Abiya Ya Rushe Shugabannin Kananan Hukumomi da Kansilolin Jiharsa
- Gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, ya umarci Ciyamomin kananan hukumomi 17, mataimakansu, da kansiloli su sauka daga mulki
- Wannan umarni na kunshe ne a wata sanarwa da Sakataren gwamnatin jihar, Chris Ezem, ya fitar ranar Jumu'a 23 ga watan Disamba, 2022
- Ciyamomi da kansilolin sun hau kan mulki ne a watan Disamban 2020 kuma wa'adinsu ya kare a wannan watan da muke ciki
Abia - Gwamnan jihar Abiya, Okezie Ikpeazu ya umarci a hanzarta rushe baki ɗaya shugabannin kananan hukumomi 17 na jihar, mataimakansu da Kansiloli.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa matakin gwamna Ikpeazu na kunshe ne a wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Chris Ezem, ya fitar ranar Jumu'a 23 ga watan Disamba, 2022.
A cewar Sakataren, gwamna ya ɗauki wannan matakin ne biyo bayan karewar wa'adin mulkinsu na tsawon shekaru biyu.
Gwamnatocin kananan hukumonin da aka rushe sun shiga Ofis ne bayan samun nasara a zaɓe a watan Disamba na shekarar 2020.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Gwamna Ikpeazu ya gode masu bisa namijin kokarin da suka yi suka bayar da lokacinsu wajen yi wa al'umma aiki kana ya masu fatan Alheri a harkokin da zasu fuskanta a gaba
Bayan haka gwamnan ya umarci su miƙa ragamar jagoranci ga shugabannin ma'aikata na yankunansu.
Kwamishinar masana'antu a jihar Abiya ta yi murabus daga mukaminta
Wannan ci gaban na zuwa ne awanni kalilan bayan kwamishinar masana'antu na jihar Abiya, Uwaoma Olawengwa, ta miƙa takardar aje aiki ga gwamna Ikpeazu.
Da take zantawa da manema labarai a Umuahia, Olawengwa ta bayyana cewa ta fice daga jam'iyyar PDP kuma ta koma jam'iyyar APGA.
Olawengwa ta bayyana cewa dalilin ɗaukar matakin sabule hannunta daga gwamnati sirri ne kuma ita kaɗai ya shafa. Tace ɗan takarar gwamnan APGA ne ya dace da jihar a 2023.
A wani labarin kuma gwamnan jihar Benuwai ya roki mazauna jiharsa su duba cancanta wurin zaɓen shugabanni a 2023
Da yake jawabi jim kaɗan bayan rattaba hannu a kasafin kuɗi, Gwamna Samuel Ortom ya shawarci mutane kar su sake kuskuren kallon jam'iyya wurin zaɓe, su duba wa zasu zaɓa.
Yace a yanzu mutane na bukatar shugabannin da zasu taimaka masu su ji tausayin kana su shawo kan matsalolinsu.
Asali: Legit.ng