Jam'iyyar PDP Ta Dakatar da Mai Magana da Yawunta a Jihar Gombe

Jam'iyyar PDP Ta Dakatar da Mai Magana da Yawunta a Jihar Gombe

  • Rikici ya sake kunno kai a jam'iyyar PDP reshen jihar Gombe, an dakatar da mai magana da yawun jam'iyyar, Murtala Usman
  • A wata sanarwa da Sakataren jiha, Alhaji Adamu Abubakar, ya fitar ranar Alhamis, yace ana zargin shi da yin zagon ƙasa
  • Da yake martani ta wayar salula, Usman yace tabbas ya samu takardar dakatarwa amma dama a shirye yake ya yi murabus

Gombe - Babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa PDP ta dakatar da mai magana da yawunta a reshen jihar Gombe, Murtala Usman, bisa zargin cin amana.

Jaridar PM News tace wannan matakin na kunshe ne a wata sanarwa da sakataren PDP na jiha, Alhaji Adamu Abubakar, ya rattaɓawa hannu kuma ya fitar ranar Alhamis a Gombe.

Jam'iyyar PDP.
Jam'iyyar PDP Ta Dakatar da Mai Magana da Yawunta a Jihar Gombe Hoto: pmnews
Asali: UGC

Sanarwan ta ce:

"A matsayinsa na jami'in hulɗa da jama'a na jam'iyya kamata ya yi a ga yana kare martabar PDP amma sai aka ga yana wasu halayya abun ban mamaki idan aka yi la'akari da manufofin jam'iyya."

Kara karanta wannan

‘Yan Sandan Borno Sun Gurfanar da Mutum 9 Kan Zargin Kaiwa Atiku Hari a Borno

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Muna sanar da ɗaukacin al'umma cewa duk wanda ya kulla wata harkalla da shi da sunan yana wakiltar PDP to ya sani fa ya sanya shi a kwana."

Na yi murabus daga kan mukamin - Usman

Da yake martani kan batun dakatar da shi, Usman a wata hira ta wayar tarho yace ya samu takardar dakatarwa ranar Alhamis 22 ga watan Disamba, 2022.

Yace tun kafin haka, ya jima yana shirye-shiryen rubuta takardar yin murabus daga mukamin gaba ɗaya.

Sakamakon haka yace a halin yanzu ya yi murabus daga mukaminsa na jami'in hulɗa da jama'a na jam'iyyar PDP reshen jihar Gombe amma yana nan matsayin mamba.

A cewarsa nan ba da jimawa ba zai fito ya bayyana matakin da ya ɗauka na gaba a siyasance inda ya kara jaddada cewa bai sauka daga yadda aka san shi na kare jam'iyyar PDP ta kowane hali ba.

Kara karanta wannan

2023: Sarkin Katsina Ya Faɗi Wanda Zai Iya Zama Shugaban Kasa Yayin da Ya Karbi Bakuncin Atiku

Kwamishina a Jihar PDP Ta Yi Murabus, Ta Sauya Sheka Zuwa APGA

A wani labarin kuma Tsagin Wike a PDP Ya Samu tangarɗa yayin da ɗaya daga cikin gwamnonin G5 ya rasa kwamishinarsa

Yayin zantawa da manema labarai a Umuahia, kwamishinar masana'antu ta jihar Abiya ta sanar da cewa ta sauka daga kan mukaminta.

Baya ga haka, tsohuwar kwamishinar tace ta fice daga jam'iyyar PDP ta koma APGA, a cewarta zata ba da gudummuwar wurin farfaɗo da jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262