Borno: ‘Yan Sanda Sun Gurfanar da Mutum 9 Kan Zargin Kaiwa Tawagar Atiku Farmaki

Borno: ‘Yan Sanda Sun Gurfanar da Mutum 9 Kan Zargin Kaiwa Tawagar Atiku Farmaki

  • Abdul Umar, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Borno, ya tabbatar da kama wasu matasa kan zarginsu da ake yi da kaiwa tawagar Atiku Abubakar farmaki
  • Kwamishinan ‘yan sandan ya sanar da cewa 12 daga cikinsu duk magoya bayan jam’iyyar APC ne yayin da 2 daga ciki ne kacal ‘yan PDP
  • Ya yabawa Gwamna Zulum kan umarnin da ya bayar na kamawa tare da gurfanar da duk wani wanda ya tada tarzoma yayin siyasa a fadin jihar

Borno - Kwamishinan ‘yan sandan jihar Borno, Abdul Umar, yace rundunar ta gurfanar da mutum 9 da take zargi da kaiwa tawagar ‘dan takarar shugabancin kasa na PDP, Alhaji Atiku Abubakar, farmaki a jihar.

Kwamishinan ‘yan sanda
Borno: ‘Yan Sanda Sun Gurfanar da Mutum 9 Kan Zargin Kaiwa Tawagar Atiku Farmaki. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kwamishinan ‘yan sandan wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Alhamis, yace jimillar mutum 14 masu tada tarzoma a yayin lamurran siyasa suka kama a jihar.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kaiwa Ayarin Dakarun Yan Sanda Hari a Arewa, An Rasa Rayuka

Daga cikin mutum 14 da ake zargin, Umar yace 12 daga ciki magoya bayan jam’iyyar APC ne yayin da sauran 2 suka kasance magoya bayan jam’iyyar PDP.

“Duk da akwai zargin cewa wani ya mutu, har a halin yanzu ba a ga gawar ba.”

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

- Yace.

Yace an dauka matakai ba kadan ba daga wurin ‘yan sanda domin dakile dabanci a jihar, Daily Trust ta rahoto.

Ya yabawa gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum da ya basu umarnin gaggawa wurin kama duk wani mutum da yake kawo hayaniya yayin kamfen, komai matsayinsa, a kai shi kotu.

Kwamishinan ‘yan sandan yace rundunar ta kama mutum 119 da ake zargi sun tafka laifuka har da bata yaran mutane da shan miyagun kwayoyi.

Zuki ta Malle: APC tayi martani kan Kaiwa Atiku farmaki a Borno

Kara karanta wannan

'Yan Sandan Sun Cika Hannu Da Manajan Cibiyar Zana Jarabawar JAMB, Bisa Zargin Salwantar Da Kwamfuwotoci 83

A wani labari na daban, jam’iyyar APC mai mulkar jihar Borno ta musnata labarin da ake yadawa na cewa ‘yan jam’iyyar APC sun kaiwa Atiku Abubakar farmaki a jihar.

Kamar yadda Sanata Dino Melaye ya bayyana, miyagun ‘yan daba sun kaiwa tawagar ‘dan takarar shugabancin kasa na PDP, Atiku Abubakar, farmaki a jihar Borno.

Sai dai a martanin jam’iyyar APC, tace wannan tsabar karya ce da aka zabga amma babu wanda ya kai musu farmaki yayin kamfen din.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng