Zaben 2023: Atiku Ya Bayyana Abin Da Zai Yi Idan Ya Sake Faduwa Zabe Bayan Yin Takara Sau 6
- Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce zama shugaban kasar Najeriya burinsa ne na tsawon rayuwar kuma zai ci gaba da kokarin cikawa burin muddin yana da karfi da lafiya
- Amma duk da haka, dan siyasan haifafan jihar Adamawa ya nuna cewa takarar shugaban kasa na 2023, takararsa na shida, ne zai zama na karshe
- Hadimin tsohon mataimakin shugaban kasar kuma ya bayyana yadda nasarar Atiku za ta samu a zaben shugaban kasa na 2023
Legas, Najeriya - Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi takarar shugaban kasa sau biyar. Takararsa na yanzu na neman gadon shugaba Buhari a 2023 shine zai zama karo na shida.
A wani hira da Financial Times ta wallafa, Atiku ya ce zama shugaban kasar Najeriya burinsa ne na rayuwa kuma zai cigaba da kokarin cika burin idan har yana da rai da lafiya.
Financial Times ta rahoto Atiku a wurin kamfen din Legas yana cewa:
"Burina ne na rayuwa kuma idan har ina da lafiya da rai, zan cigaba da kokarin cika burin."
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Na zo mataki na karshe, In ji Atiku
Bayan cewa zai cigaba da kokarin neman cika burinsa na zama shugaban kasa idan har yana da rai da lafiya, Atiku ya yi gagawar nuna cewa wannan takarar ne zai zama na karshe, rahoton Financial Times.
Ya ce:
"Na zo mataki na karshe yanzu. Bana tunanin bayan wannan karon zan sake takara."
Yadda Atiku zai ci zaben shugaban kasa a 2023
A bangare guda, tsohon hadimin dan takarar shugaban kasa wanda ba a bayyana sunansa ba ya fada wa FT cewa dan takararsa zai ci zaben 2023.
Hadimin ya ce Atiku zai yi galaba a kan abokan hamayarsa, Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC, da Peter Obi na LP a kudancin Najeriya kuma zai samu kuri'u sosai a arewacin Najeriya saboda Shugaba Muhammadu Buhari ba ya takara ba.
An yanke wa matashi daurin shekaru 2 a gidan yari saboda lalata allunan tallan kamfen din Atiku
Wata kotu da ke zamanta a Bukuru, jihar Filato ta yanke a wani matashi dan shekara 20, Gabriel Orupou hukuncin daurin shekara biyu a gidan gyaran hali.
Alkalin kotun Hycinth Dolnaan, amma ya bawa Orupou zabin biyan tarar N100,000 bisa laifin da aka same shi da aikatawa na lalata allunan tallar shugabancin kasa na Atiku Abubakar na PDP.
Asali: Legit.ng