Matsala a Gidan Kwankwaso, Ɗan Takarar Mataimakin Gwamna Ya Yi Murabus

Matsala a Gidan Kwankwaso, Ɗan Takarar Mataimakin Gwamna Ya Yi Murabus

  • New Nigerian Peoples Party watau NNPP ta yi babban rashin jigonta yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2023
  • John Bahago, ɗan takarar mataimakin gwamna a jihar Neja a inuwar jam'iyyar ya janye daga takara, ya fice daga NNPP
  • Tsohon jigon NNPP bai bayyana musabbabin ɗaukar wannan matakin ba kuma bai faɗi jam'iyyar da ya yanke komawa ba

Niger - Gabanin babban zaɓen 2023, ɗan takarar mataimakin gwamna a inuwar NNPP mai kayan marmari a jihar Neja, John Bahago, ya hakura da takara kuma ya fice daga jam'iyyar.

Wannan matakin da ɗan siyasan ya ɗauka na ƙunshe ne a wata wasiƙa da ya tura wa shugaban NNPP na gundumar Guni, ɗauke da kwanan watan 14 ga watan Disamba, 2022.

Rigima a NNPP.
Matsala a Gidan Kwankwaso, Ɗan Takarar Mataimakin Gwamna Ya Yi Murabus Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Daily Nigerian ta tattaro cewa tsohon mamba a majalisar dokokin Neja ya gode wa jam'iyyar bisa goyon bayan da ta nuna masa har ya zama abokin gamin ɗan takatar gwamna, Yahaya Ibrahim Sokodeke.

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyar NNPP Ta Yi Babban Kamu a Arewa, Dubbunnan 'Ya'yan PDP Sun Sauya Sheka Zuwa Cikinta

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa Mista Bahago, bai fadi dalilin da yasa ya fice daga NNPP ba yayin da ya rage makonni a fafata zaben 2023.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shin dagaske Kwankwaso na shirin janye wa Atiku takara a 2023?

A wani cigaban, jam'iyyar NNPP ta ƙasata musanta raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa tana gab da kulla ƙawance da babbar jam'iyyar hamayya ta ƙasa wato PDP.

Jam'iyyar ta yi wannan ƙarin bayani ne yayin martani kan wani rahoto da ake jinginawa Sakataren kwamitin amintattu, Injiniya Buba Galadima, wanda ya yi ikirarin da yuwiwar haɗa karfi da PDP.

Sai dai a wata sanarwa da Sakataren watsa labarai na NNPP ta ƙasa, Meho Agbor, ya fitar, yace sam babu wannan shirin a ƙasa.

Melaye Da Wasu Yan PDP Sun Yi Watsi Da Rade-radin Cewa Gwamnonin G5 Na Bayan Tinubu

Kara karanta wannan

Dalilin da Zai Sanya Na Marawa Peter Obi Baya a Zaɓen 2023, Kakakin Dattawan Arewa

A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP ta musanta rahoton cewa gwamna Wike da sauran yan tawagarsa sun yanke mara wa Tinubu baya a 2023

Hadiminan ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PDP sun ce har yanzun ana ci gaba da tattaunawar neman sulhu don ɗinke kowace irin ɓaraka.

An jima ana kai kawo a jam'iyyar PDP tsakanin tsagin Atiku da kuma G5 bisa jagorancin gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262