Bidiyon Yadda Matar Atiku Abubakar Ta Girgiza Intanet, Tace 'Ku Zabi APC'

Bidiyon Yadda Matar Atiku Abubakar Ta Girgiza Intanet, Tace 'Ku Zabi APC'

  • Matar ɗan takarar shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, watau Titi Abubakar ta girgiza kafafen sada zumunta
  • A wani Bidiyo da yanzu haka yake yawo an ji Titi na cewa kowa ya karɓo katin zabensa ya zabi APC a watan Fabrairu
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan mai gidanta, Atiku Abubakar ya buga ta shi baranɓaramar a Jos, babban birnin Filato

Wani Bidiyo dake yawo na Titi Abubakar, Uwar gidan ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, tana kiran 'yan Najeriya su zaɓi jam'iyyar APC ya girgiza Intanet.

A cikin bidiyon wanda aka ji Titi na caccakar jam'iyyar APC bisa jefa mutane cikin yunwa da wahalar rayuwa, ta buga subutar baki a fili, ta faɗa wa magoya baya su zaɓi APC a 2023.

Kara karanta wannan

2023: "Muna Faɗin Allah a Baki" Gwamnan Arewa Ya Magantu Kan Sauya Shekar Sakatarensa Zuwa PDP

A kalamanta, Titi ta ce:

"A ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023, kowa ya hito, idan ka san baka karɓo katin zaɓe PVC ba, to ka garzaya ta karɓo PVC, ya kamata dukkanmu mu zaɓi APC."
"Jam'iyyar APC ta ɗaukar mana alƙawurran abubuwa da yawan gaske a ƙasar nan amma yanzun muna ganin halin da muka tsinci kan mu a ciki."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jam'iyyar APC ta yi martani

Da yake tsokaci kan Bidiyon, mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaɓen Tinubu/Shettima, Festus Keyamo, ya yi kokarin kare matar Atiku.

Keyamo ya wallafa shafinsa na Tuwita cewa:

"Ba da jimawa ba matar Atiku watau Titi Abubakar ta roki 'yan Najeriya zau zaɓi APC a ranar 25 ga watan Farbarairu, 2023."
"Maganar gaskiya wannan subutar harshe ne, amma a wurin mu, babu wani abun wulaƙantawa idan mace ta aikata haka, musamman idan ta yi hnazarin gyara kuskuren."

Kara karanta wannan

2023: "Ka Ci Zaɓe Ka Ci Zabe" Yadda Dubun Dubatar Magoya Baya Suka Yi Maraba da Tinubu a Jihar Arewa

A wani labarin kuma Gwamna Soludo Ya Fada wa Atiku cewa yana ɗaya daga cikin mutum biyu na sahun gaba a zama shugaban ƙasa a 2023

A makonnin da suka shige, Chukwuma Soludo, ya yi ikirarin cewa ba ya ga waɗan nan biyun sauran duk 'yan ta yi daɗi ne kawai da yan wasan dirama.

Ya faɗi haka ne a gidan gwamnatinsa da ke Awaka, ranar Alhamis lokacin da Atiku ya kai masa ziyara kafin zuwa filin kamfe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262