Jam'iyyar NNPP tayi babban kamu a jihar Gombe, ta amshi magoya bayan PDP

Jam'iyyar NNPP tayi babban kamu a jihar Gombe, ta amshi magoya bayan PDP

  • Jam'iyya mai kayan marmari wato NNPP tayi wani babban kamu a jihar Gombe, arewa maso gabashin Najeriya
  • Ɗan takakar gwamna a jam'iyyar, Khamisu Mailantarki ya amshi dubunnan masu sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP
  • Ya buƙace su da su cigaba da tallatawa da samarwa da jam'iyyar magoya baya a jihar gabanin 2023

Ɗan takarar gwamnan jihar Gombe a ƙarkashin inuwar jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Khamisu Mailantarki, ya amshi dubunnan ƴaƴan jam'iyyar PDP.

Ɗan takarar gwamnan ya dai tarbi shugabanni da mambobin ƙungiyar Sardauna Dawo-Dawo, wacce take ta magoya bayan PDP.

Ya dai amshi waɗanda suka sauya sheƙar daga PDP zuwa NNPP a Gombe, a ranar Juma'a. Rahoton jaridar The Punch ya tabbatar

Dan takarar gwamnan NNPP ya amshi magoya bayan PDP a jihar Gombe.
Jam'iyyar NNPP tayi babban kamu a jihar Gombe, ta amshi magoya bayan PDP
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Dalilin da Zai Sanya Na Marawa Peter Obi Baya a Zaɓen 2023, Kakakin Dattawan Arewa

Shugaban jam'iyyar NNPP na jihar Abdullahi Maikano, shine ya ƙarbe su a hukumance.

Ƙungiyar ta Sardauna Dawo-Dawo, ta sauya sunan ta zuwa tafiyar Mailantarki bayan sauya sheƙar inda take cewa ta yanke shawarar marawa ɗan takarar NNPP baya saboda mutum ne "matashi, ya cancanta, mai jini a jika da kirki."

Shugaban ƙungiyar Muhammad Makson ya bayyana cewa:

Ɓallewar mu daga goyon bayan PDP mataki ne wanda muka yanke a tare, dukkanin mu mun yanke shawarar tafiya sannan mu koma NNPP domin mu samu shugabanci mai kyau a jihar Gombe.
Mun aminta cewa Mailantarki yana da hali mai kyau da ƙwarewar da zai ceto jihar Gombe daga mulkin rashin kataɓus na APC.
Mutum ne wanda a baya ya riƙa faɗin abubuwan da suka dace sannan yayi abubuwan da suka kamata.

Shugaban ya bayyana cewa ƙungiyar tana da shugabanni kusan 2000 da mambobi 20,000 a cikin mazaɓu 114 na jihar Gombe.

Kara karanta wannan

2023: "Muna Faɗin Allah a Baki" Gwamnan Arewa Ya Magantu Kan Sauya Shekar Sakatarensa Zuwa PDP

Da yake tarbar su zuwa jam'iyyar NNPP, Mailantarki ya tabbatar musu da cewa za a riƙa damawa da su a dukkanin lamuran jam'iyyar.

Musamman yanzu da aka buga kugen yaƙin neman zaɓe, sannan Insha Allah, NNPP zata lashe babban zaɓe dake tafe.

Ya buƙace su da su cigaba da tattarowa jam'iyyar magoya baya sannan su tallata ƴan takarar ta a jihar.

2023: Kana Cikin Yan Takara Biyu Na Sahun Gaba Dake Neman Gaje Buhari, Soludo Ga Atiku

A wani labarin kuma Gwamna Soludo na Anambra Ya gana da Atiku, ya faɗa masa yana cikin waɗanda zasu iya gaje Buhari a 2023

Idan baku manta ba a watan Nuwamban da ya gabata, gwamnan yace mutum biyu ne ke neman shugaban ƙasa a 2023, sauran duk yan wasan kwaikwayo ne.

Atiku Abubakar ya ziyarci gwamnan har gidan gwamnati sa'ilin da jirgin yakinsa ya dira Anambra ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262