Abinda Zai Sa Na Mara Wa Peter Obi Baya a 2023, Kakakin Dattawan Arewa
- Kakakin ƙungiyar Dattawan Arewa ya faɗi dalilin da zai sanya ya goyi bayan takarar Peter Obi
- Baba-Ahmed yaya ne ga ɗan takarar mataimakin shugaban kasa a inuwar Labour Party watau Datti Baba-Ahmed
- Ya nuna shakkun sa game da yiwuwar zaɓe a wasu yankunan ƙasar nan a babban zaben 2023 mai zuwa
Babban darektan watsa labarai da wayar da kai na ƙungiyar dattawa Arewa (NEF), Dr Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana abinda ka iya sanya wa ya marawa takarar Peter Obi da Datti baya
Hakeem Baba-Ahmed yace zai marawa ƴan takarar baya ne kaɗai idan har sune waɗanda suka fi cancanta a takarar shugabancin ƙasar nan a zaɓen 2023, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.
Dr Hakeem ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Channels TV a shirin su na Siyasa a Yau.
Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party, Dr Yusuf Datti Baba-Ahmed, ƙani ne a wajen Hakeem Baba-Ahmed.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A kalaman sa:
“Zan goyi bayan Peter Obi da ƙani na ne kaɗai idan sune 'yan takarar da suka fi cancanta. Kasan ina aiki kan wani shiri da dattawan Arewa, wanda yaba dukkanin ƴan takarar dama iri ɗaya.
Abinda zai hana wasu mutane zaɓe a 2023 - Hakeem
Ya ƙara da cewa ƴan Najeriya da dama ba za su samu damar yin zaɓe ba saboda matsalar rashin tsaro, ko saboda hukumar zaɓe mai zaman kanta ta INEC ba zata iya kai kayan zaɓe ba ko mutane ba zasu iya yin zirga-zirga ba.
Ya ƙara da cewa:
Akwai gagarumar matsala wacce dole a magance ta yadda ya dace. Idan kayi duba zuwa yankin Kudu maso Gabas, 'yan awaren IPOB, y'an bindigan da ba'a san ko su wanene ba."
2023: "Ka Ci Zaɓe Ka Ci Zabe" Yadda Dubun Dubatar Magoya Baya Suka Yi Maraba da Tinubu a Jihar Arewa
"Su na farmakar mutane inda suke cin karen su ba babbaka. An hana mutane zaɓe saboda wasu tsirarun mutane na ƙona ofisoshi da kayayyakin hukumar INEC.
Tana Neman Karewa Atiku, Wasu Gwamnonin PDP Sun Fara Shirin Komawa Bayan Tinubu a 2023
A wani labarin kuma Wasu rahotanni daga makusantan gwamnonin G5 sun nuna cewa da yuwuwar Wike ya kulla kawance da Tinubu a 2023
Wike mai jan tawagar wacce ta kunshi gwamnoni da kusoshin PDP sun shata layin cewa har sai Ayu ya sauka zasu mara wa Atiku Abubakar baya.
An rasa zaman lafiya a tsakanin ƙusoshin PDP ne tun bayan kammala zaɓen fidda gwani wanda gwamna Wike ya sha ƙasa a hannun Atiku.
Asali: Legit.ng