Kotu Ta Jingine Hukuncin Haramtawa Baki Ɗaya 'Yan Takarar APC a Ribas Shiga Zaven 2023
- Jam'iyyar APC ta yi nasara a Kotun ɗaukaka ƙara game da haramta wa 'yan takararta shiga zaben 2023 a jihar Ribas
- Kwamitin alkalai uku na Kotun ɗaukaka ƙara sun jingine hukuncin babbar kotun tarayya, sun tabbatar da sahihancin zaɓen fidda gwanin APC
- Wannan hukunci zai baiwa baki ɗaya yan takarar APC a jihar su ci gaba da harkokin yakin neman zabe gadangadan
Rivers - Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Patakwal, ta soke hukuncin babbar Kotun tarayya, ta tabbatar da sahihancin 'yan takarar jam'iyyar APC a jihar Ribas.
Leadership ta tattaro cewa da yake yanke hukunci Alkalin babbar Kotun tarayya, Mai shari'a, Emmanuel Obile, yace APC ba ta bi matakan doka ba wurin zaɓen Deleget masu kaɗa kuri'a a wurin zaɓen fidda gwani.
Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci
Kwamitin alkalai uku na Kotun ɗaukaka ƙara karkashin mai shari'a Muhammed Lawal-Shaibu yace George Orlu da sauran mutum uku ba su bi matakan cikin gida ba kafin shigar da ƙara a Kotu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yace waɗanda ake kara sun gaza shiga zaben fidda gwanin jam'iyya sabida haka ba su da hurumin ɗaukar matakin zuwa Kotu.
A cewar alƙalin zaben Deleget ɗin da zasu yanke wanda zai takara a jam'iyyun siyasa wani abu ne da ya shafi harkokin cikin gida saboda haka Kotu ba ta da ikon tsoma baki.
Daga nan sai Mai shari'a Lawal Shaibu ya jingine hukuncin da Kotun baya ta ɗauka kan APC, kana ya tabbatar da sahihancin matakan zaɓen fidda gwani.
Bugu da ƙari, Alkalin ya kuma umarci a biya N500,000 a kowane Kes daga cikin guda uku a matsayin kuɗin wahalar ɗaukaka kara ga jam'iyyar APC, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Yan Najeriya Sun Samu Sabon Sumfurin Shugaba Buhari, Doguwa Ya Jaddada Wanda Ya Dace da Mulki a 2023
A wani labarin kuma Babbar Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Karar da Ta Nemi Rushe Takarar Tinubu da Atiku a 2023
Tsohon ƙaramin ministan ilimi da ƙungiyar kare hakkin ɗan adam da ake kira RAI a takaice ne suka shigar da ƙarar. Sun nemi a haramtawa Atiku Takara kana a maye gurbin Tinubu da tsohon ministan.
Sai dai da Kotu ke yanke ƙara yau Alhamis, 15ga watan Disamba, 2022 tace masu shigar da ƙarar ba su ikon haka, sannan ta rushe ƙungiyar RAI.
Asali: Legit.ng