IGP Yana Ganawa da Kwamishinonin 'Yan Sanda Kan Gabatowar Zabe

IGP Yana Ganawa da Kwamishinonin 'Yan Sanda Kan Gabatowar Zabe

  • A halin yanzu, sifeta janar na 'yan sanda, Usman Alkali Baba yana ganawa da kwamishinonin 'yan sanda da sauran shugabannin 'yan sanda a Abuja
  • Hakan ya biyo bayan da sifeta-janar din ya nemi ganawa da jami'an a hedkwatar tsaro a Abuja don shiryawa gangamin zaben 2023
  • Kwamishinonin 'yan da sauran masu ruwa da tsaki ne suka samu damar halartar ganawar don ganin yadda zasu tabbatar da tsaro a zabe me karatowa

FCT, Abuja - Sifeta-janar na 'yan sanda, Usman Alkali Baba, yanzu haka yana ganawa da kwamishinonin 'yan sanda da shugabannin yankunan 'yan sanda a Abuja don shiryawa gangamin zaben shekarar 2023 gami da tabbatar da tsaro a cikin kasa, jaridar Punch ta rahoto.

Sifeta Janar Alkali
IGP Ya Gana da Kwamishinonin 'Yan Sanda Kan Gabatowar Zabe. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Suna ganawar tsaron ne a hedkwatar jami'an tsari, inda kwamishinonin 'yan sanda da mataimaka sifetocin 'yan sanda da mataimaka shugabannin yankunan 'yan sanda da sauran jami'an masu ruwa da tsaki suka halarta.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng