"Ƙa Ci Zabe Ka Ci Zabe" Yadda Dubun Dubatar Mutane Suka Tarbi Tinubu a Neja

"Ƙa Ci Zabe Ka Ci Zabe" Yadda Dubun Dubatar Mutane Suka Tarbi Tinubu a Neja

  • Jam'iyyar APC da jirgin yakin neman zaɓen shugaban kasa sun dira jihar Neja ranar Laraba 14 ga watan Disamba 2022
  • A gangamin kamfen APC, Bola Tinubu bai samu damar yin cikakken jawabi ba sakamakon yadda magoya baya suka cika maƙil
  • Idan baku manta ba Tinubu da abokin takararsa Kashim Shettima sun je Kaduna ranar Litinin inda suna kaddamar da kamfen Arewa ta yamma

Niger - Dandazon magoya baya sun cika maƙil ba masaka tsinke a Trade Fair Complex dake Minna, wurin da jam'iyyar APC ta gudanar da gangamin yakin neman zabe ranar Laraba.

A wata sanarwa da Ofishin Midiyan Tinubu ya fitar ɗauke da sa hannun Tunde Rahman kuma aka aike wa Legit.ng Hausa ranar Laraba, an ce mutanen sun taru ne domin ganin ɗan takarar APCn kawai.

Kamfen Tinubu a Neja.
"Ƙa Ci Zabe Ka Ci Zabe" Yadda Dubun Dubatar Mutane Suka Tarbi Tinubu a Neja Hoto: APC
Asali: Facebook

Dubun dubatar magoya bayan sun samu damar ganin mai neman zama shugaban kasa a APC jim kaɗan bayan ya kammala gana wa da manoma da yan kasuwar hatsi a Minna.

Kara karanta wannan

An Nemi Bola Tinubu An Rasa Ana Tsakiyar Kamfe, APC Ta fito Tayi Karin Haske

Yadda suka tarbi Tinubu

Yayin da ɗan takarar ya isa filin gangamin, dubbannin mahalarta sun tashi suna faɗin, "Asiwaju, ka ci zaɓe ka ci zaɓe, kar kace komai," suka mamaye wurin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ganin wannan tsantsar soyayya da goyon baya da fatan Alheri, Bola Tinubu, ya miƙa godiya garesu bisa nuna masa a shirye suke su kaɗa masa kuri'unsu.

Tinubu ya bayyana murna a fili

Tsohon gwamnan Legas ɗin, wanda ya shiryo jawabinsa na musamman, dole ta sanya ya jingine shi, ya bayyana farin ciki da murnarsa game da yadda masoya suka nuna ana tare.

Gangamin ya samu halartar ɗan takarar mataimaki, Kashim Shettima da wasu gwamnonin APC da suka haɗa da Abubakar Bello na Neja, Atiku Bagudu na Kebbi da Abubakar Badaru na Jigawa.

Sauran sun haɗa da, Babajide Sanwo-Olu na Legas, Babagana Zulum na Borno, Abdullahi Sule na Nasarawa, Abdullahi Ganduje Kano, da Simon Lalonga na Filato, Darakta Janar na Kamfe.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya Sun Samu Sabon Sumfurin Shugaba Buhari, Doguwa Ya Jaddada Wanda Ya Dace da Mulki a 2023

Tsoffin gwamnoni irin su Abdul'Aziz Yari na jihar Zamfara, Adams Oshiomhole na Edo da sauran jiga-jigai da dama sun samu halartar wurin.

Atiku Zai Gana da Gwamnan Wata Jam'iyya da Sarakuna, PDP Ta Fara Kullin Shawo Kan Su Wike

A wani labarin kuma jirgin ɗan takarar shugaban kasa na PDP zai dira jihar Anambra gobe, ya shirya zama gwamna Soludo

A wata sanarwa da Darakta Janar da kwamitin kamfen Atiku/Okowa ya fitar, yace Atiku zan gudanar da muhimman taruka a ziyarar da zai kai Anambra.

Budu ɗa ƙari, yace PDP ta sake kafa tawaga ta musamman da zata ƙara jaraba yunkurin rarrasa tsagin gwamna Wike da ake kira G5.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262