Kotun Daukaka Kara Ta Yi Watsi da Karar Dake Kalubalantar Nasarar Sanata Uba Sani a Zaben Fidda Gwanin APC
- Dan takarar gwamnan jam'iyyar APC a jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya tsallake rijiya da baya yayin da aka bashi gaskiya a kotu
- Abokin hamayyarsa a zaben fidda gwanin gwamna, Sani Sha'aban ya maka APC a kotu a zargin an yi magudi a zaben
- A yau dai kotun daukaka kara ta raba gardama, ta ce Uba Sani ne dan takarar gwamnan APC a jihar Kaduna
FCT, Abuja - Kotun daukaka kara mai zamanta a Abuja ta yi watsi da karan da Sani Sha’aban ya shigar kan nasarar dan takarar gwamnan APC na Kaduna, Sanata Uba Sani a zaben fidda gwanin gwamnan jam’iyyar da aka gudanar a jihar.
Legit.ng ta ruwaito cewa, yayin soke karar, kotun ta ce ta fahimci cewa, daukaka karar an yi ta ne ba bisa ka’ida ba, kuma bata cika abin da ake bukata na cancanta ba.
Sha’aban ya daukaka kara ne kan hukuncin da babbar kotun tarayya mai zama a Kaduna ta yanke a ranar 4 ga watan Nuwamba, wacce ta yi watsi da kalubalantar zaben fidda gwanin, inda tace babu makama ko tushen gaskiya a batun.
Bai saduda ba, Sha’aban ya daukaka kara zuwa kotun daukaka da ke zama a Abuja.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Barista Sule Shuaibu, wanda shine lauyan APC ya tabbatar da cewa, an yanke hukuncin da ya ba Uba Sani gaskiya a zaben fidda gwanin da aka gudanar, zai ci gaba da rike tutar APC a matsayin dan takarar gwamna har zuwa zaben 2023.
Alkalai uku na kotun daukaka karan ne suka yi zaman yanke hukunci a yau Laraba 13 ga watan Disamba.
Asali: Legit.ng