Jerin Jihohin da Tabbas Atiku Zai Ci Zabe a 2023, Inji Jigon PDP Reno Omokri
- Tsohon hadimin tsohon shugaban Najeriya, Reno Omokri ya yi hasashen jihohin da dan takarar shugaban kasan PDP, Atiku zai lashe a zaben 2023 a cikinsu ba tare da wata matsala ba
- Reno mazaunin kasar Ingila kuma jigon PDP ya ce Atiku zai kawo akalla kaso 25% daga jihohin da bai yi musu cin kaca ba a zaben
- Jihohin da Omokri ya hango Atiku zai lashe sun hada da Adamawa, Gombe, Taraba, Nasarawa, Neja da Benue
Burtaniya, kasar Ingila – Reno Omokri, jigon jam’iyyar adawa ta PDP ya bayyana jerin wasu jihohi da yake da yakinin dan takarar PDP, Atiku Abubakar zai lashe kuri’unsu gaba daya a zaben 2023.
Omokri, wanda tsohon hadimin tsohon shugaban kasan Najeriya Goodluck Jonathan ne ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter kamar yadda Legit.ng Hausa ta samo.
A cewarsa, Atiku za iyi nasara a jihohin da bai cinye su akalla ko da kaso 25% ne zai kawo a zaben na 2023 mai zuwa.
Ga jerin jihohin da Atiku zai iya cin zabe ba makawa a cewar Reno Omokri.
1. Kano
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
2. Delta
3. Katsina
4. Akwa-Ibom
5. Kaduna
6. Kuros Riba
7. Jigawa
8. Bayelsa
9. Sokoto
10. Edo
11. Zamfara
12. Filato
13. Kebbi
14. Bauchi
15. Adamawa
16. Gombe
17. Taraba
18. Nasarawa
19. Neja
20. Benue
Atiku ba irin Tinubu bane, inji Omokri
A tun farko, Reno Omkori ya ce Atiku mutum ne mai tsafta idan aka kwatanta shi da sauran 'yan takarar da ke da burin gaje kujerar Buhari.
A cewarsa, babu wani abin da ake zargin Atiku dashi sabanin yadda ake kai ruwa rana don sanin tushen arzikin dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu.
Ya ce ba a taba tuhumar Atiku da wani laifin cin kudin kasa ko ta'ammuli da kwaya ba, kuma kowa yasan inda yake samun kudinsa na halal.
A bangare guda, matar Atiku ta ce ya kamata mata a yankin Kudu maso Yamma su yi ganganin zaben mijinta a zaben 2023.
A fahimtarta, wannan ne karon farko da za a samu mace ta zama 'First Lady' daga yankin kasancewarta 'yar Kudu.
Ana ci gaba da tallata 'yan takara gabanin zaben 2023, inda za fafata tsakanin jam'iyyun siyasa daban-daban.
Asali: Legit.ng