Hotunan Yakin Neman Zaben Atiku/Okowa Na Yau A Jihar Nasarawa
Jirgin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party PDP, ya yada zango jihar Nasarawa, Arewa maso tsakiyar Najeriya ranar Litinin, 12 ga watan Disamba.
Garin Lafiyar Bare-Bari, babbar birnin jihar Nasarawa ya cika ya banbatse yau Litnin da manyan jigogin jam'iyyar ta PDP.
Dan takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023 karkashin inuwar PDP, ya dira Nasarawar ne tare mataimakinsa, Ifeanyi Okowa da Shugaban uwar jam'iyyar, Iyorchia Ayu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Bayan taron, Atiku ya fitar da jawabin godiya ga Sarkin Lafiya bisa kyakkyawan tarbar d ayayi musu.
Yace:
"Musamman ina godiya ga jawaban Sarkin bisa doguwar alakata da fadar."
"Ina godiya bisa tarbar da na samu daga wajen Sarkin Lafiya, HRH Justice Sidi Muhammadu Bage I (CFR)"
"A taron kamfenmu, na jaddada niyyar samawa matasanmu aiki da kuma taimakawa yan kasuwa masu karamin karfi a jihar Nasarawa da fadin kasar."
Kalli hotunan taron:
Hutun rana 1 kawai sukayi
A ranar Asabar, Atiku da jigogin PDP sun yi taron kamfensu a birnin tarayya Abuja.
Uwar jam'iyyar PDP a shafinta na Tuwita ta bayyana cewa lokaci yayi da Alhaji Atiku Abubakar da Gwamna Ifeanyi Okowa zasu kwato Najeriya daga hannun jam'iyyar APC.
Asali: Legit.ng