Wani Jigo A Jam'iyyar PDP a Jihar Gombe Ya Koma Jam'iyyar APC Mai Mulkin Jihar
- Jam'iyyar PDP mai adawa a jihar Gombe ta rasa wani mai dubban magoya baya a jihar zuwa jam'iyyar APC
- Jigon jam'iyyar PDP wanda akewa lakabi da Gwamna sabida jama'arsa yace jam'iyyar PDP a Gombe bata yiwa magoya bayanta adalci
- Fitar Gwamna daga jam'iyyar PDP a jihar Gombe ya sauyawa 'ya'yan jam'iyyar PDP a Gombe lissafin siyasarsu
Gombe: Dr. Jamil Isyaku Gwamna, jigo a jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) a jihar Gombe ya koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) tare da dubban magoya bayansa.
Dr. Jamil gwamna ya bada sanarwar sauya shekar tasa ne tare da magoya bayansa a jiya Juma'a a Gombe yayin da yake zantawa da manema labarai, ciki harda jaridar Daily Trust.
Gwaman ya nuna rikicin cikin gida, rashin shugabanci, rashin bin doka da oda a cikin jam’iyyar da rashin hadin kai a matsayin dalilin da ya sa ya yanke shawarar ficewa daga PDP.
A cewarsa, shugabancin jam’iyyar PDP a jihar ya yi wa jam’iyyar mummunar riko wajen tafiyar da al’amuran jam’iyyar wanda ya haifar da samar da bangarori daban-daban a jam’iyyar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ce akidar siyasarsa ta dogara ne kan hadin kai, daidaito da adalci, yana mai yace:
"Idan ba a samu wadannan a cikin jam’iyyar ba to babu dalilin zama a wannan a cikinta"
Gwamna wanda kuma shi ne Sardaunan Gombe ya ce PDP ba za ta iya tafiyar da jihar Gombe ba da yadda take fifita son rai akan maslaha al'umma.
"A cikin siyasa, dimokuradiyyar cikin gida na da matukar mahimmanci kuma idan ba za ku iya gano hakan ba, to aiwatar da mulkin dimokuradiyya a kan jama'ar gari da wanda ba 'yan jam'iyyar mu bazai yiwuba"
Mai Jamilu Gwamna Ya Gani A Jam'iyyar APC
Gwamna ya ce jam’iyyar APC ta fi kowace jam’iyya tsari a Gombe kuma tana tafiyar da al’amuranta yadda ya kamata kamar kace iyali daya ne.
Ya yi kira ga magoya bayan sa da su hada kai da goyon bayan jama’a a fadin jihar domin ganin jam’iyyar APC ta ci gaba da rike jihar da kuma samun tazarar kuri’u fiye da wanda aka samu a 2019.
Asali: Legit.ng