2023: Dan Takarar Majalisar Tarayya Ya Kwanta Dama Bayan Halartar Taro
- Ɗan takarar mamban majalisar wakilan tarayya a mazaɓar Atisbo/Saki East/Saki West karkashin inuwar Accord Party ya rasu.
- Rahotanni sun nuna cewa ɗan siyasan, Jacob Funmi Ogunmola, ya rasu ne bayan halartar wani taro da ya isa a makare a garin Saki
- An ce Ogunmola ya ce baya jin daɗin bayan kammala taron, nan da nan tawagarsa suka maida shi gida a Legas, rai ya yi halinsa
Oyo - Jacob Funmi Ogunmola, mai neman zama mamba a majalisar wakilan tarayya mai wakiltar mazaɓar Atisbo/Saki East/Saki West a inuwar Accord Party, ya riga mu gidan gaskiya.
Jaridar The Nation ta tattaro cewa, Ogunmola, tsohon shugaban ƙaramar hukumar Atisbo ta jihar Oyo yace ga garinku nan bayan halartar wani taro a garin Saki.
Rahotanni sun bayyana cewa ɗan siyasan ya rasa rayuwarsa ne bayan an maida shi gidansa dake jihar Legas.
Abinda ya faru tun a wurin taron
Wata majiya tace jim kaɗan bayan kammala taron a Saki, Ɗan siyasan ya fara maganar ba ya jin daɗin jikinsa. A cewar majiyar hakan ya tilasta aka ɗauke shi zuwa gida a Legas.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A wani sako da ya saki a shafinsa na dandalin sada zumunta watau Facebook, ɗan takarar majalisar tarayyan ya faɗa wa waɗanda suka shirya taron cewa ba halinsa bane zuwa wuri a makare.
A cewarsa, yana fama da wata matsala ne shiyasa ya isa wurin a makare kana ya basu hakurin faruwar hakan.
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa a wasu 'yan watanni da suka wuce, wanda ya gaji kujerar Jacob Funmi Ogunmola a ƙaramar hukumar Atisbo, Wasiu Owolabi, ya rasa ransa a wani hatsarin mota da ya rutsa da shi.
Dan Takarar Majalisar Tarayya a Inuwar Jam'iyyar PDP Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Osun
A wani labarin mai kama da wannan, jam'iyyar PDP mai jan ragamar jihar Osun ta rasa ɗaya daga cikin 'yan takarar majalisar tarayya a zaben 2023
Mista Sola Arabambi, ɗan takarar PDP a mazaɓar Irewole/Isokan/Ayedaade ta tarayya yace ga garinku nana ranar Asabar da ta gabata bayan fama da rashin lafiya ta ɗan lokaci.
Tuni dai abokanan siyasa, yan uwa da abokanan arziki suka fara tura sakonnin ta'aziyya ga iyalan mamacin tare da masa addu'ar samun salama.
Asali: Legit.ng