2023: LP, NNPP, ADP Sun Caccaki Dogara Kan Yadda Kunngiyarsu Ta Zabi Atiku A Matsayin Dan Takara
- Kungiyar Kiristocim Arewa Ta Marawa Atiku Abubakar Baya A Zaben 2023 Bayan Da Kungiyar Tace Ta gama tuntuba
- Matakin Da Su Dogara Suka Dauka Ya Bar Baya Da Kura Inda Da Dama Daga Cikin Kungiyoyi Da Dai-Daiku ke sukar lamarin Nasu
- A Satin Da Ya Gabata Ne Kungiyar Addinai da Masu Fada Aji A Arewa Tasu Yakubu Dogara Ta Marawa Dan Takarar Jam'iyyar PDP Baya.
Abuja: Ofishin yada labarai na Jam'iyyun LP, NNPP da ADP, sun yi Allah wadai da Abinda kungiyar shugabannin kiristoci da musulmi suka yi a Arewacin kasar nan, na marawa dan takarar shuugaban kasan PDP baya.
Jam'iyyun sunce basu yi mamkin irin yadda kungiyar su Dogaran marawa Atiku baya ba, inda suka bayyana hakan a matsayin wani abin takaici.
Jam'iyyun sunce dole ne su maidawa Dogara martani, sabida yadda suka nuna san kai ko kuma rashin dattako a matsayinsu na shuwagabbin al'umma da bai kamata su nuna bangaranci ba.
A cikin sanarwa da jam'iyyar LP ta fitar wanda Obi da Baba Suke mata takarar tace zasu ci zabe ko ba goyan bayansu. kamar yadda jaridar Vanguard ta rawaito
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sannarwa ta kara da cewa a matsayin dogara na wanda ke da hakkin marawa duk wanda ya ga dama baya ba wanda ya isa ya hanashi, to amma amfani da sukai da kungiyarsu, suka siyasantar da ita shine matsala
Sanarwar ta ci gaba cewa:
“A bayyane yake, tsohon kakakin ya san cewa shi shugaba ne kuma yana cikin wanda ake jin magnar su a fannin shugabancin al'umma to mai zai hana ace su tsaya a tsakayia ba tare da zabar bari ba, dan ganin an kawo ci gaba mai dorewa."
2023: Baba-Ahmed Ya Fasa Kwai, Ya Fadi Yan Takarar Shugaban Kasa 2 da Ba Zasu Iya Kashe Kudin da Suka Tara Ba
“Muna sanar da Dogara kan ya sani yawancin al’ummar Najeriya sun hau jirgin neman mafita daga halin da kasar nan ta shiga wanda kuma su wanda suka marawa bayan, yana cikin wanda suka jefa kasar a halin da ta ke ciki".
“Dogara wanda lokacin yana gudanar da Shugabancin Majalisar Wakilai ya yi nasarar gudanar da majalisa inda ya baiwa kowanne bangaren dama, ba nuna wariya ko adawa, to mai zai hana ace yanzu ya goyi bayan Peter Obi wanda shima yayi irin wannan a lokacin da yake gwamna"
Sanarwar bata gushe ba sai da ta tabo batun yadda yan kasa sukai amanna da yadda aka dauko kananan jam'iyyu wanda ake ganin sune zasu magance matsalar kasar .
Daga karshe sanarwa tace:
“Mu a matsayin mu na yan jam'iyyar LP muna ganin rashin dacewar abinda su Dogaran sukai, wanda suna ganin gaskiya suka ki mara mata baya, tare da dauko wanda suka san bazai fitar da kasar daga halin da ta ke ciki ba.”
Ba mu yi mamakin Matsayar kungiyar Kiristocin Arewa ba karkashin jagorancin Dogara — Inji NNPP da ADP
Da yake zantawa da jaridar Vanguard kan wannan batu, shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Farfesa Rufa’i Ahmed Alkali, ya ce jam’iyyar tayi takaici tare da mamakin abinda su Dogaran suka yi.
A cewar Alkali, jam’iyyar za ta mayar da martani ga kungiyar da yaren da za ta fahimta.
Ya ce:
“Mun samu Sanarwar da kungiyar tayi. Mun ji takaici amma haka ba zai zo da wani bakon lamari ba. A abinda zamu fada musu kawai shine za mu mayar musu da martani sosai cikin yaren da za su fahimta.”
Shima da yake zantawa da jaridar Vanguard, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar ADP, Yabagi Sani, ya ce lokaci ya yi da ‘yan Najeriya za su duba cancanta a matsayin ma’aunin zabar shugabanni a Najeriya, maimakon addini, kabilanci da kuma yanki.
Sani, wanda kuma shi ne dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar , ya ce:
“Bai kamata a mayar da Najeriya kasar addini, kabilanci ko yanki ba, a daina irre-ire wadannan abubuwa dan ganin an magance abun da yake damun mu a kasar nan mai makon batun kabilanci, addini ko yanki."
“Jam’iyyar mu ta ADP a karkashin jagoranci na, kuma dan takarar shugaban kasa tana da dukkan abin da ya kamata a zabe ta sabida tanade-tanade da taiwa ilimi, lafiya da sauransu”
Asali: Legit.ng