Gaskiya ta bayyana: Ainahin jadawalin albashin shugaba Buhari zuwa na gwamnonin kasar nan

Gaskiya ta bayyana: Ainahin jadawalin albashin shugaba Buhari zuwa na gwamnonin kasar nan

Yawan kudin da manyan gwamnatin Najeriya ke dauka ya kasance abun tattaunawa a tsakanin yan Najeriya a koda yaushe, wanda hakan kan sa ata ikirari marasa tushe.

Yayinda mafi akasarin yan Najeriya ke ganin yan siyasan kasar na kwasan manyan albashi sama da abunda ya kamata ace suna dauka a wata, a koda yaushe yan siyasan ma kan yi kokarin kare kansu akan abunda suke dauka.

Misali, sabon shugaban majalisar dattawa kuma shugaban majalisar dokoki, Ahmed Lawan, kafin zabensa, ya kare zargin naira miliyan 13.5 da aka ce ana biyan kowani sanata duk wata a kasar.

Lawan yace babban bangare na kudin alawus na gudanar da ayyuka ne. Yace ba za a rage yawan kudin ba cewa babu wani abu mai kama da garabasa a kudin da ake biyan sanatocin tunda kowannensu na tashi ne da naira miliyan daya duk wata da alawus da ayyuka.

Nawa ne gaskiyar abunda zababbun yan syasan Najerya ke karba? Legit,ng tayi bincke akan albashin duk wata da alawus din Shugaban kasar Najeriya, mataimakin Shugaban kasa, gwamnonin jihad a mataimakan gwamnoni suke karba.

Shugaban kasar Najeriya

A bisa ga takardar da hukumar tattara kudin shiga ta RMAFC ta shirya sannan ta wallafa a shafin bpsr.gov.ng, a duk shekara Shugaban kasa Muhammadu Buhari na tafiya gida da N14,058,820:00 ciki harda alawus (N14.0m).

Shugaban kasar na karba N1,171,568:20 (N1.17m) duk wata.

Gaskiya ta bayyana: Ainahin jadawalin albashin shugaba Buhari zuwa na gwamnonin kasar nan
Rababen albashi da alawus din shugaban kasa
Asali: UGC

Mataimakin Shugaban kasar Najeriya

A bisa ga takardar, mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo na karban 12,126,290:00 (N12.1m) duk shekara yayinda albashinsa na wata ya kasa 1,010,524:16 (N1.01m).

Gaskiya ta bayyana: Ainahin jadawalin albashin shugaba Buhari zuwa na gwamnonin kasar nan
Albashi da alawus din mataimakin shugaban kasa
Asali: UGC

Gwamnonin jiha

Gwamnonin jiha na Najeriya na karban N7,782,967:50 (N7.78m) duk shekara yayinda suke karban N648,580:62 duk wata.

Gaskiya ta bayyana: Ainahin jadawalin albashin shugaba Buhari zuwa na gwamnonin kasar nan
Ainahin jadawalin albashin gwamnonin kasar
Asali: UGC

Mataimakan Gwamnoni

Ga mataimakan gwamnoni, a shekara suna karban N7,392,752:50 (N7.39m) inda a wata suke karban N616,062:69.

Gaskiya ta bayyana: Ainahin jadawalin albashin shugaba Buhari zuwa na gwamnonin kasar nan
Ainahin jadawalin albashin mataimakan gwamnonin
Asali: UGC

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel