Babbar Kotu Ta Rushe Zaben Fidda Ɗan Takarar Gwamna a Jihar Abiya
- Kotun tarayya mai zama a birnin Abuja ta rushe zaben fidda ɗan takarar gwamna na jam'iyyar APGA a jihar Abiya
- Alkalin Kotun, mai shari'a Binta Nyako, tace ta gamsu an tafka kura-kurai a zaben ta umarci jam'iyyar ta sake gudanar da sabo cikin mako biyu
- Daya daga cikin 'yan takarar da suka nemi tikitin ne ya garzaya Kotu yana mai kalubalantar nasarar Mista Greg Ibe
Abuja - Babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja ta soke zaben fidda gwanin jam'iyyar APGA na takarar gwamnan jihar Abiya wanda ya gudana ranar 29 ga watan Mayu, 2022.
Alkalin Kotun mai shari'a Binta Nyako, wacce ta sanar da hukuncin Kotu ta kuma umarci jam'iyyar ta sake shirya sabon zaɓen fidda gwani cikin kwanaki 14.
Mai Shari'a Nyako ta yanke wannan hukuncin ne a ƙarar da Chikwe Udensi ya shigar gaban Kotun, yana kalubalantar sakamakon zaben.
Channels tv ta tattaro cewa Greg Ibe ne ya samu nasara a zaben fiddda gwanin amma ɗaya daga 'yan takarar ya kalubanci nasarar da ya samu a Kotu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Alkalin ta bayyana cewa bayanan da shaidu suka gabatar mata, ta gamsu cewa zaben fidda ɗan takarar gwamnan jihar Abiya a inuwar APGA, wanda ya gudana a watan Mayu kewaye yake, "murdiya da saba wa ka'ida."
Mista Udensi ya sha kaye a hannun Mista Ibe a zaben da jam'iyyar APGA ta shirya da sa idon INEC amma ya nuna bai yarda ba, ya garzaya Kotu a bi masa haƙƙinsa.
Bayanai sun nuna cewa Chikwe Udensi, ya roki Kotu ta dawo masa da nasarar da yake ganin ya yi, ta ayyana shi a matsayin halastaccen ɗan takarar gwamna karkashin inuwar APGA.
Ya kuma roki Kotun idan haka bata samu ba ta rushe zaɓen kana ta umarci jam'iyyar ta shirya sabon domin a sake fafatawa gaskiya ta yi halinta, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Ɗan Tsohon Gwamna Ya Lashe Zaben Fidda Gwanin APC Da Aka Canza a Ondo
A wani labarin kuma Jam'iyyar APC ta gudanar da sabon zaben fidda gwani a mazaɓar ɗan majalisar tarayya a jihar Ondo
An canza sabon zaɓen ne bayan rigingimun da suka biyo na farko da APC a gudanar a watan Mayu, lamarin da ya kai ga zuwa Kotu.
A sabon zaɓen ɗan tsohon gwamnan jihar Ondo, Adebayo Adefarati, ya samu nasarar doke sauran 'yan takara da kuri'u 71.
Asali: Legit.ng