2023: PDP Ta Sanar da Sakamakon Sabon Zaben Fidda Gwanin da Ta Canza a Bauchi
- Garba Dahiru, ɗan takarar da ya lashe zaben fidda gwanin PDP a mazaɓar Sanatan Bauchi ta kudu ya sake samun nasara
- Babbar kotun tarayya dake zama a Owerri, jihar Imo ta rushe zaben kuma ta umarci PDP ta shirya sabo
- Takaddamar bayan zaɓen fidda gwani na daya daga matsalolin da suka hana jam'iyyar PDP zama lafiya a matakin ƙasa
Bauchi - Ɗan takarar da ya lashe zaben fidda gwanin farko na takarar Sanatan Bauchi ta kudu karkashin inuwar PDP, Alhaji Garba Ɗahiru, ya sake nasara a sabon zaben da jam'iyyar ta shirya.
Idan baku manta ba babbar Kotun tarayya mai zama a Owerri, jihar Imo ta rushe zaben fidda gwanin farko kana ta umarci a sake sabon zaɓe tsakanin wanda ya yi nasara da mai biye masa, Mahiru Maiwada, wanda ya nuna rashin gamsuwa.
Tribune ta ruwaito cewa an gudanar da sabon zaɓen ne ranar Laraba a ɗakin Taron Banquet dake Zaranda Hotel and Tower karkashin sa idon Sakatariyar PDP ta ƙasa.
Sakamakon sabon zaben da aka gudanar
Da yake sanar da sakamakon zaɓen, shugaban kwamitin shirya zaben, Sanata Muhamed Bello, ya ayyana cewa Garba Ɗahiru ya tashi da kuri'u 211 ya doke abokin hamayyarsa Mahiru Maiwada mai kuri'u 7.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A jawabinsa ga manema labarai jim kaɗan bayan sanar da sakamakon, Ɗahiru yace nasarar da ya samu a yanzu ta nuna sahihanci zaben da aka gudanar tun farko.
Ya yi kira da sauran 'yan takara da su zuba wa zuciyarsu ruwan sanyi su riƙa hakuri kuma su ba da haɗin kai wurin aiki tare domin nasarar PDP a zaben 2023.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa Garba Ɗahiru ne kaɗai ya halarci wurin zaben yayin da Alhaji Mahiru da sauran 'yan takara waɗanda sunayensu suka fita a jikin kuri'a duk basu hallara ba.
Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Bauchi, Hamza Koshe Akuyam, ya yaba da yadda aka yafiyar da zaben lami lafiya inda ya jaddada cewa PDP a dunkule take.
Kotu Ta Rushe Zaben Fidda Gwanin Jam'iyyar APC Na Takarar Sanata
A wani labarin kuma Babbar Kotun Tarayya dake Awka ta rushe zaɓen da ya samar da Ifeyinwa Anazonowu a matsayin yar takarar Sanatan Anambra ta arewa a inuwar APC.
Alkalin Kotun yace lokacin da aka gudanar da zaben, wacce aka ce ta yi nasara ba ta zama cikakkiyar mamba mai rijista ba a APC kuma da kanta tace ta janye daga takara.
Bayan haka Kotu ta bayyana Nelson Onubogu a matsayin halastaccen ɗan takara kana ta umarci INEC ta rattaɓa sunansa a cikin masu neman takara a 2023.
Asali: Legit.ng