Kotu Ta Rushe Zaben Fidda Gwanin Jam'iyyar APC Na Takarar Sanata
- Babbar Kotun tarayya mai zama a Awka ta soke zaben fidda gwanin jam'iyyar APC na mazaɓar Sanatan Anambra ta arewa
- Alkalin Kotun mai shari'a Muhammad yace wacce aka ayyana a matsayin yar takara ba mambar APC bace kuma ta janye
- Jam'iyyar APC na fama makamantan irin waɗannan rikice-rikice da suka biyo bayan zaɓen fidda gwani a sassan ƙasar nan da dama
Anambra - Babbar Kotun tarayya mai zama a Awka, a ranar Talata ta rushe zaben fidda gwanin da ya samar da Misis Ifeyinwa Anazonowu a matsayin yar takarar Sanatan Anambra ta arewa a inuwar APC.
Jaridar Tribune Online ta ruwaito cewa Alkalin Kotun mai shari'a Muhammad ne ya karanta hukuncin da Kotun ta yanke a Awka, babban birnin jihar.
Alkalin ya ayyana zaɓen da ya fitar da Misis Anazonowu a matsayin yar takara a mazaɓar sanatan da, "Saba wa doka, mara amfani kuma abin watsar wa."
Kotun ta yanke cewa ta gamsu da bayanan da suka nuna wacce aka ce ta lashe zaben sam ba mambar APC bace tun farko kuma bisa raɗin kanta ta sanar da janyewa daga takara tun kafin ranar zaɓe.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Shin APC ta rasa ɗan takara a mazabar kenan?
Bugu da ƙari, Kotun ta bukaci jam'iyyar APC da hukumar zabe INEC su karɓi injiniya Nelson Onubogu a matsayin halastaccen ɗan takarar Sanata a mazaɓar Anambra ta arewa.
Ta kuma umarci INEC ta sanya sunan Onubogu a matsayin ɗan takarar Sanata a inuwar APC sakamakon wacce ake ƙara, Misis Anazonowu ba ta zama cikakkiyar mamba ba kuma zaɓenta zagaye yake da karya doka.
Haka zalika mai shari'a Muhammed ya umarci wacce ake ƙara ta biya Injiniya Nelson Onubogu miliyan ɗaya kuɗin da ya ɓannatar.
A wani labarin kuma Kotu ta amince zata bayar da belin shugaban tsagin jam'iyyar APGA, Chief Edozie Njoku
A ranar Litinin ɗin da ta gabata, Kotun ta umarci a iza keyar shugaban jam'iyyar bisa zargin haɗa takardar hukuncin Kotun koli na ƙarya.
An gurfanar da Njoku tare da shugaban matasan APGA bisa zargin sun haɗa takardar umarnin Kotu na karya domin nuna kansu a matsayin shugabannin jam'iyyar.
Asali: Legit.ng