2023: Ɗan Tsohon Gwamna Ya Lashe Zaben Fidda Gwanin APC Da Aka Canza a Ondo

2023: Ɗan Tsohon Gwamna Ya Lashe Zaben Fidda Gwanin APC Da Aka Canza a Ondo

  • Jam'iyyar APC reshen jihar Ondo ta gudanar da sabon zaɓen fidda gwani a wata mazaɓar ɗan majalisar wakilan tarayya
  • Sakamakon zaben ya nuna cewa, Adebayo Adefarati, ɗa ga tsohon gwamnan jihar ne ya lashe zaɓen da kuri'u 71
  • Tun bayan gudanar da zaben fidda gwanin mazaɓar a watan Mayu, rikici da shiga Kotu suka biyo baya, aka yi sulhun canza sabo

Ondo - Adegboyega Adefarati ya lashe sabon zaben fidda gwani wanda jam'iyyar APC ta shirya na ɗan takarar mamban majalisar wakilan tarayya mai wakiltar mazabar Akoko ta kudu-Gabas/Akoko ta kudu-yamma daga jihar Ondo.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Mista Adegboyega, ɗa ne ga tsohon gwamnan jihar Ondo, Adebayo Adefarati, wanda ya yi mulki tsakanin 1999 zuwa 2003.

Adegboyega Adefarati.
2023: Ɗan Tsohon Gwamna Ya Lashe Zaben Fidda Gwanin APC Da Aka Canza a Ondo Hoto: thenation
Asali: UGC

Jam'iyyar APC ta canza zaɓen fidda ɗan takarar ne bayan wasu daga cikin 'yan takara sun kai ƙarar jam'iyya Kotu, inda suka ƙalubalanci yadda aka gudanar da zaɓen a watan Mayu.

Kara karanta wannan

Tinubu, Obi Ko Kwankwaso? Gwamna Wike Ya Magantu Kan Wanda Mutanensa Zasu Zaba a 2023

Bugu da ƙari, baya ga 'yan takara wasu daga cikin Deleget ɗin wucin gadi da ke kaɗa kuri'a, sun shigar da ƙara Kotu suna neman a rushe zaɓen saboda wasu dalilai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganin an taro ta ta ko ina, wasu shugabannin APC suka jagoranci zaman sulhu da 'yan takara wanda daga ƙarshe aka cimma matsayar shirya sabon zaɓe.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa bayan haka Kotu ta umarci jam'iyyar APC ta sake sabon zaɓen fidda gwani a mazaɓar cikin kwanaki Bakwai.

Yadda sakamakon zaɓen ya kasance

A sabon zaɓen fidda gwanin da aka shirya, Mista Adefarati ya samu kuri'u 71 ya lallasa abokin hamayya da yazo na biyu, Dr. Olusegun Ategbole, wanda ya tashi da kuri'u 55.

Adefarati, ya yi kira ga 'ya'yan jam'iyyar APC a mazaɓar da su maida wuƙarsu kube kana su zo a haɗa hannu a yi aiki domin kai jam'iyya ga nasara a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

2023: APC Ta Hargitse a Jihar Arewa Yayin da Wani Sanatan Jam'iyyar Ya Gana da Ɗan Takarar PDP

Shugaban APC na jihar Ondo, Injiniya Ade Adetimehin, ya roki mambobin jam'iyya su mara wa 'yan takararsu tun daga sama har ƙasa baya a zaɓen 2023.

A wani labarin kuma Shugaban kwamitin Kamfen Atiku Abubakar yace tabbas jam'iyyar PDP ta tafka kuskure a abubuwan dake faruwa

Gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, wanda ke jagorantar tallata Atiku, yace rigingimun da ke faruwa a PDP wata alama ce mai nuna babu kamar jam'iyyar a faɗin Afirka.

Emmanuel yace dama zaman tare ya gaji haka amma yana da tabbacin za'a warware matsalar kafin ranar zaɓen shugaban kasa a watan Fabrairu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262