Jam’iyyar Da Bata Damu Da Rayuwar Jama’a Ba: Surukin Buhari Ya Fice Daga APC

Jam’iyyar Da Bata Damu Da Rayuwar Jama’a Ba: Surukin Buhari Ya Fice Daga APC

  • Jam'iyyar APC ta rasa daya daga cikin yan takararta na gwamna a jihar Kaduna, Sani Mahmood Sha'aban
  • Sha'aban wanda suruki ne ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rasa tikitin takarar gwamnan APC a hannun Sanata Uba Sani
  • Tsohon jigon na APC ya bayyana dalilinsa na barin jam'iyyar kuma ya magantu kan mataki na gaba da zai dauka

Kaduna - Honourable Sani Mamood Sha'aban, surukin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sauya sheka daga jam'iyyar All Progreasives Congress (APC) gabannin babban zaben 2023, Daily Trust ta rahoto.

Sha'aban ya nemi takara a zaben fidda dan takarar gwamna na APC a jihar Kaduna amma ya sha kaye a hannun Sanata Uba Sani.

Sani Mahmood Sha'aban ya fice daga APC
Jam’iyyar Da Bata Damu Da Rayuwar Jama’a Ba: Surukin Buhari Ya Fice Daga APC Hoto: Isyaku Suleiman
Asali: Facebook

Ya kalubalanci nasarar Sani a kitu amma kuma ya sake shan kaye. Kotun ta yi watsi da shari'ar, tana mai cewa bata da hurumin sauraronta.

Kara karanta wannan

Da Gaske Jam'iyyar PRP Ta Rushe Cikin APC a Sakkwato? An Fayyace Gaskiyar Lamari

Dalilin da yasa na bar APC, Sha'aban ya magantu

A ranar Litinin, 28 ga watan Nuwamba, Sha'aban ya sanar da ficewarsa daga APC a cikin wata wasika da ya sanyawa hannu, Daily Trust ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daraktan kwamitin kamfen dinsa, Barista Joshua Danladi Elhraim, ne ya karanto wasikar a wani taron manema labarai.

Ya ce harkokin jam'iyyar ne suka sanha shi yin murabus, yana mai zargin cewa maimakon shayar da mutane romon damokradiyya, wasu yan tsiraru a APC reshen Kaduna sun kwace tsarin jam'iyyar.

Ya ce:

"A inda ra'ayoyin yawancin mutane bai da wani muhummanci. Ba zan iya ci gaba da kasancewa a jam'iyyar da bata damu da rayuwar mutane, zaman lafiya da mutunta al'ada ba.
"Ni Sani Mahmood Sha'aban na yi murabus daga matsayin dan APC a dukkan matakai a hukumance a yau 28 ga watan Nuwamban 2022."

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari Ya Yi Murna Yayin da Kwankwaso Ya Yi Babban Rashi a NNPP

Zan sanar da mataki na gaba da zan dauka

Sha'aban ya ce yanzu yana tattaunawa don daukar mataki na gaba, cewa zai sanar da jam'iyyar da zai koma nan ba da jimawa ba.

Ya ce zai ci gaba da kalubalantar dan takarar gwamnan APC a kotu duk da cewar ya fice daga jam'iyyar.

Babu mai iya daukar ran Tinubu, Fani-Kayode

A wani labari na daban, kakakin kungiyar yakin neman zaben Asiwaju Bola Tinubu, Femi Fani-Kayode ya bayyana dan takarar shugaban kasar na APC a matsayin kainuwa dashen Allah.

Tsohon ministan ya ce babu wani mutum da zai iya karbar ran Tinubu kafin ko bayan zaben 2023 sai Allah wanda ya busa masa rai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng