Ba Dai Mutum Ba Sai Allah: Jigon APC Ya Ce Babu Mai Iya Kashe Tinubu Kafin Ko Bayan 2023

Ba Dai Mutum Ba Sai Allah: Jigon APC Ya Ce Babu Mai Iya Kashe Tinubu Kafin Ko Bayan 2023

  • Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya ce duk wani kulla-kulla da ake yi kan Bola Tinubu ba zai yi tasiri ba
  • Fani-Kayode ya yi gargadin cewa babu wani mutum mai numfashi da zai iya kashe dan takarar shugaban kasar na APC a zaben 2023
  • A cewar tsohon ministan, Allah kadai ne ke da ikon daukar ran kowani bawansa a lokacin da ya so

Kakakin kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Femi Fani-Kayode, ya bayyana cewa babu wani mutum da zai iya kashe dan takarar jam'iyyar, Asiwaju Bola Tinubu.

A wata wallafa da yayi a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, 27 ga watan Nuwamba, tsohon ministan sufurin jirage na kasar, ya bayyana cewa Allah kadai ke da ikon yin haka.

Kara karanta wannan

'Allah Ya Baka Lafiya' Kwamitin Kamfen Din Atiku Ya Maida Martani Ga Subul da Bakan Tinubu

Fani-Kayode da Tinubu
Ba Dai Mutum Ba Sai Allah: Jigon APC Ya Ce Babu Mai Iya Kashe Tinubu Kafin Ko Bayan 2023 Hoto: Bola Tinubu, Fani-Kayode
Asali: Facebook

Da yake jadadda cewar Allah ne kawai zai iya daukar ran bawansa, tsohon ministan ya ce babu wani mahaluki da zai iya kashe Tinubu kafin ko bayan babban zaben 2023.

Tsohon gwamnan na jihar Lagas dai ya bayyana a yayin gangamin kamfen dinsa a jihar Lagas cewa babu mai iya kashe shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk wani kulli da ake yi kan Tinubu ba zai cimma nasara ba

Da yake jadadda matsayin Tinubu game da rayuwarsa, Fani-Kayode ya ce babu abun da zai samu dan takarar na APC kafin ko bayan zabe mai zuwa.

Ya bayyana a shafinsa:

"Akwai wani tsoro da zan taba a yanzu. Kuma shine tsoron cewa wani abu zai iya faruwa da Asiwaju Bola Tinubu a yayin ko bayan zaben.
"Kamar yadda ya fadi a gangamin kamfen, makiyansa da masu zaginsa ba za su iya kashe sa ba, muna nan daram a kan wannan batu kuma muna sanar da shi a dare da rana. Ba za a iya tsare Asiwaju ba, ba za a iya garkame shi ba, ba za a iya soke zabensa ba, ko kuma a iya kashe shi.

Kara karanta wannan

Jihar Kano Da Wasu Jihohin Arewa 5 Da Nike Da Tabbacin Zan Lashe: Tinubu

"Masu daukar wannan mugun nufi na mutuwa ga dan takararmu, ku mutane ne kuma baku wuce haka ba. Ku ba komai bane kuma ba za ku iya yin komai ba. Allah kadai ke ba da rai kuma shi ke daukar kayansa."

Kwamitin yakin neman zaben Atiku ta yi martani ga barambaraman Tinubu

A gefe guda, kakakin kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar, Sanata Dino Melaye ya yiwa Tinubu addu'an samun lafiya bayan ya yi subul da baka a wajen gangamin kamfen dinsa na jihar Lagas.

Tinubu ya bukaci magoya bayansa da su je su karbi katin APV dinsu maimako PVC da zai ce sai kuma ya gyara maganarsa zuwa APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng