Wike Ya Fadi Abun da Ya Wakana Tsakanin Atiku Da Jonathan Kafin Zaben 2015

Wike Ya Fadi Abun da Ya Wakana Tsakanin Atiku Da Jonathan Kafin Zaben 2015

  • Jagoran gwamnonin G5, Nyesom Wike ya tuna yadda Atiku Abubakar ya ki marawa Goodluck Jonathan a zaben 2015
  • Gwamnan na jihar Ribas wanda ya zargi Atiku da muzanta tsohon shugaban kasar duk da ya yi tattaki ya bisa har Landan
  • Wike ya ce sharadin da tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayar shine cewa Jonathan ya hakura da tikitinsa

Rivers - Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya roki tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da ya goya masa baya domin ya zarce a zaben 2015 amma sam yaki bayar da hadin kai.

Wike ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 21 ga watan Nuwamba, lokacin da Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi ya kaddamar da hanyar Akpabu-Itu-Umudiogha a karamar hukumar Emohua ta jihar Ribas, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shin Atiku Zai Yi Sulhu Da Boko Haram? Ɗan Takarar Na PDP Ya Bayyana Abinda Ke Zuciyarsa

Jonathan, Atiku da Wike
Wike Ya Fadi Abun da Ya Wakana Tsakanin Atiku Da Jonathan Kafin Zaben 2015 Hoto: The Nation
Asali: UGC

A cewar Wike, Jonathan ya yi tattaki har otel din Dorchester da ke Landan don ganawa da Atiku tare da rokonsa ya dawo jam'iyyar don ya mara masa baya, jaridar The Nation ta rahoto.

Sai dai kuma, maimakon haka, Wike ya ce tsohon mataimakin shugaban kasar ya nemi Jonathan ya hakura da tikitinsa a 2015.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wike, wanda yayi takarar zaben fidda dan takarar shugaban kasa na PDP a watan Mayu, ya ce shi bai nemi Atiku ya janye masa a matsayin dan takarar shugaban kasa na 2023 ba.

Ya ce, maimakon haka ya nemi Atiku ya tabbatar da tsige Iyorchia Ayu daga matsayin shugaban PDP na kasa don dan kudu ya maye gurbinsa.

Jonathan, dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2015, ya sha kaye a hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari na APC a lokacin da ya so zarcewa kan kujerarsa.

Kara karanta wannan

Rudani: Gwamnan PDP ya yi watsi da Atiku, ya ce Kwankwaso yiwa kamfen a jiharsa

Atiku da abokin takararsa, Ifeanyi Okowa, sun ziyarci Jonathan a gidansa na Abuja a ranar 17 ga watan Nuwamba domin magance rikicin da ya dabaibaye PDP amma har yanzu ba a ji komai daga tsohon shugaban kasar ba.

Yayin da zaben 2023 ya rage saura watanni uku, akwai fargabar cewa rikicin Wike da Atiku kan rashin saukar Ayu zai shafi damammakin da dan siyasan na Adamawa ke da shi a zaben.

Wike da sauran gwanonin PDP biyar wadanda aka fi sani da G5 ko 'Integrity Group' na so Ayu ya sauka daga kujerarsa saboda cewar arewa ta yi kane-kane a cikin jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng